Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta shirya tsafa don fara amfani da wata sabuwar fasahar zamani wajen gano masu ɗaukar nauyin ta’addaci da yadda kuɗi ki shege da fice a hannun ƴan ta’adda.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya sanar da hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan gano masu ɗaukar nauyin ta’addaci a yankin Arewa maso Gabas da ƙungiyar CISLAC ta shirya wanda ya samu ɗaukar nauyin GIABA-ECOWAS.
- Buga Kudi: EFCC Za Ta Sake Gurfanar Da Emefiele A Kotu A Ranar Laraba
- Da Ɗumi-ɗumi: EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Da ‘Yarsa A Gobe Alhamis
Olukoyede, ya bayyana damuwarsa kan yadda ɗaukar nauyin ta’addaci ke dukar wani sabon salo. Ina tabbatar da cewa EFCC ta gano wasu kafafe ba wai iya Binance ba da ake amfani da su wajen hada-hadar aikewa ƴan ta’adda kuɗi, kuma har an kulle asusu sama da guda dubu.
Ya ce, babban ƙalubalen da ke gaban su shi ne su kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa maso Gabas sakamakon yadda yaƙi ci yaƙi cinyewa, kuma sun samu wata sabuwar fasahar zamani da za su iya gano duk masu zuba kuɗi don ɗaukar nauyin ta’addaci.
“Mu a EFCC, muna damuwa da yadda har yanzu waɗannan ƴan ta’addar ke iya samun kuɗi su aiwatar da ta’addacinsu, su sayi makamai da sauransu, har su iya yin ƙarfin da suke yaƙi da sojojin Nijeriya.”
Shugaban ya kuma bayar da misalin wata da ake kira da Mama Boko Haram wacce ake mata kallon wata mai shiga tsakani amma ashe tana da hannu dumu-dumu a cikin sha’anin ta’addanci, yanzu haka tana zaune a gidan gyaran hali.