Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na baiwa kowane yaro da ke zaune a jihar ilimi kyauta tun daga matakin firamare har sakandare da na makarantar sakandire ta karantar da fasaha da sana’a.
Gwamnatin ta bayyana cewa, takardar da tafito daga ma’aikatar ilimi zuwa ga shugabannin makarantu kan karbar kudaden makaranta, ta sabawa manufofin gwamnati.
Don haka, Gwamna Nasir El-Rufai, ya bayar da umarnin soke takardar da ma’aikatar ilimi ta tura zuwa ga shugabannin makarantu, mai kwanan wata 1 ga Nuwamba, 2022, da gaggawa, sannan a mayar da duk wasu kudaden da aka karba daga hannun daliban makarantar nan take.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro na majalisar zartaswa ta jihar Kaduna da aka gudanar a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba, 2022, inda ya kara bayyana samar da ilimi kyauta na tsawon shekaru 12 na karatu a matsayin wani babban nasibi da gwamnatin ta gada kuma za ta tabbatar.
Wata sanarwa da mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, ya sanyawa hannu a ranar Talata, ta ce gwamna el-Rufai ne da kansa ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta jihar, wacce ta haramta biyan kudaden PTA da sauran kudaden haraji a makarantun gwamnati. Takardar ta tabbatar da cewa manufar ilimi kyauta a jihar, shine iyaye su hutu da bani-bani na kananan haraji da makarantu ke amsa a baya.