Wasan farko da Endrick ya daɗe yana muradin bugawa a Madrid ya kasance cikin mintuna 10 kacal amma tuni ɗan wasan na ƙasar Brazil ya taka rawar gani.
Ɗan wasan gaba na Brazil ya dai amince zai koma Real a watan Disambar 2022, amma saboda dokokin FIFA da suka hana ‘yan wasa ‘yan kasa da shekaru 18 tsallakawa zuwa kasashen ketare ya sa ya koma Real a watan Yulin bana.
- Ko Zuwan Mbappe Zai Dusashe Tauraruwar Bellingham A Real Madrid?
- Shin Barcelona Da Atletico Madrid Zu Su Iya Dakatar Da Real Madrid A La Liga?
Endrick ya canji Kylian Mbappe a minti na 86 a wasa tsakaninsu da Real Valladolid inda ya jefa kwallo a mintunan ƙarshe na wasan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp