Bayan kammala zanga-zangar EndSARS wanda ya gudana a wasu sassa na kasar nan, shugaban Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Muhammad Babandede ya ziyarci Jihar Inugu a wani bangare na rangadin da yake yi domin duba yanayin barnar da aka yi wa hukumar.
A yayin ziyarar, Babandede ya bukaci zaratan jami’an hukumar da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kishin ci gaban kasa.
Lokacin da yake horon shugabanin tsaro da sauran hukumomi masu bayar da agaji a kan su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin kwariwa, ya gargade su da su kiyaye take hakkin ‘yan kasa ko da kuwa sun tsokane su, inda ya yaba wa jami’an da ba sa nuna bambamci da kuma martaba rayuka a kowani lokaci.
Da ya isa fadar gwamnatin jihar ta Inugu kuwa, CGI Muhammad Babandede ya jinjina wa Gwamna Lawrence Ifeanyi Ugwuanyi bisa goyon bayan da ya bai wa hukumar ta shige da fice kafin zanga-zangar da bayan barnar da aka yi mata a jihar. Musamman ya gode masa saboda maye na’urar rarraba lantarki da aka barnata da kuma wasu motocin aiki da ya bai wa hukumar domin kara inganta tsaro da sintirin jami’ai.
Sanarwar da ta fito daga Jami’in yada labaru na NIS, DCI Sunday James, ta bayyana cewa, da yake mayar da jawabi, Gwamna Ugwuanyi ya yaba wa shugaban hukumar ta NIS bisa kasancewarsa jarumin dan kasa da kuma irin nasarorin da ya samar ga kasa a matsayinsa na jami’in gwamnati.