Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta nada dan kasar Holland, mai shekara 52, don maye gurbin kocin rikon-kwarya Ralf Rangnick a karshen kakar wasar nan. Hag ya zana wantaragin shekara uku, amma yana da zabin tsawaita kwangilarsa da shekara daya.
Man United ta ce nadin nasa ya ta’allaka ne da samun bizar aiki a Ingila. Rangnick, wanda ya zama kocin kungiyar bayan ta kori Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamba, zai koma matsayin mai bayar da shawara ga kocin kungiyar.
“Babban abin alfahari ne da aka nada ni a matsayin kocin Manchester kuma na yi matukar shiryawa don tunkarar kalubalen da ke gabana. Na san tarihin wannan babbar kungiyar da kuma kaunar da magoya bayanta suke mata, kuma zan zage dantse wajen samar da tawaga wacce za ta yi nasara. ” In ji Hag.