Evra Ya Koma Westham

Football Soccer - Euro 2016 - France News Conference - Clairefontaine, France - 30/6/16 - France's Patrice Evra attends a news conference. REUTERS/Charles Platiau

Kungiyar kwallon kafa ta Westham United ta dauki tsohon dan wasan Manchester United, Patrice Evra kan yarjejeniyar karshen kakar bana bayan sun yi wata doguwar tattaunawa akan yarjejeniyar.

Evra dan kwallon tawagar kasar Faransa mai shekara 36, ba shi da kungiya tun bayan da ya raba gari da Marseille, sakamakon yi wa magoyin bayan kungiyar kafa a lokacin da kungiyar za ta buga  gasar Europa.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta dakatar da shi buga wasannin gasar har zuwa karshen kakar shekarar nan, amma zai iya buga fafatawar wata kasa yayin da Marseille din kuma ta kore shi gaba daya daga kungiyar.

Dan wasan mai tsaron baya, ya buga tamaula karkashin mai koyarwa Dabid Moyes a lokacin da ya horar da Manchester United a shekara ta 2013 zuwa 2014

Evra ya bar Manchester United ya koma kungiyar Jubentus da murza-leda a shekarar 2014, bayan da ya yi shekara uku a Italiya ne ya koma Marseille ta faransa a Janairun shekara ta 2017.

Dan kwallon ya buga wa Manchester  United wasanni 379 tsakanin shekarar 2006 zuwa 2014, inda ya lashe manyn kofi tara ciki har da gasar firmiya data Zakarun Turai a shekarar 2008.

Sannan kuma ya wakilci kasarsa ta faransa wasanni a gasanni daban daban har ila yau tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Monaco ne.

Exit mobile version