Ci gaba
Mataki na Uku na Hassada:
Shi ne mutum ya so samun ni’ima kamar yadda wani yake da ita, ba tare da yana so ta gushe daga hannun wanda yake da ita ba. Wannan kuwa ba hassada ba ce, sai dai ana kiranta da fatan alheri ga kai.
Wannan nau’i na hassada ana kiran sa da ‘ al-Gibɗatu’ wata kalma ce ta Larabci da ke nufin gasa ta gari ko fatan samun alheri kamar na wani, ba tare da fatan ni’imarsa ta gushe daga hannunsa ba. Wannan hali ne da ya sha bamban da mummunar hassada wanda ke da mummunan tasiri a cikin zuciya da al’umma. Irin wannan fatan alherin Allah Ya zaburar da bayinsa a cikin Suratul Muɗaffifin aya ta 26.
Rabe-raben Irin Wannan Hassada:
1. Gibɗa a cikin Addini:
Wannan ya ƙunshi yin gasa a ibada kamar sallah, ko azumi, ko karatun Alƙur’ani, da sadaka, ko mutum ya so ya zama hamshaƙin mai kuɗi da zai rinƙa taimaka wa addini da bayin Allah. Ko kuma mutum ya nemi ya zama malami ko jagora a addini don ya koyar da mutane.
2. Gibɗa a cikin Duniya:
Wannan shi ne mutum ya so samun ilimi irin na wasu don ya amfanar da kansa da al’umma. Ko kuma son ya zama attajiri ko ɗan kasuwa ko mai wata sana’a da zai rinƙa ba wa mutane horo saboda ya ga wani yana yi shi ma ya so ya ƙware ya taimaka domin samun lada a wurin Allah. Haka nan son samun shugabanci mai kyau domin jagorantar al’umma bisa gaskiya.
Manzon Allah (SAW) ya nuna irin wannanhassadarba laifi ba ce, inda ya ce: “Babu hassada sai a cikin abubuwa biyu: mutumin da Allah Ya ba shi ilimi, sai ya yi aiki da shi yana koyar da mutane, da kuma mutumin da Allah Ya ba shi dukiya, sai ya kashe ta a cikin hanyar da ta dace.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
Bambanci Tsakanin Hassada da Gibɗa:
Idan mutum ya ga wani yana da ilimi, sannan ya so ya zama kamar shi ba tare da yana son ilimin wancan ya gushe ba, to wannan ita ce gibɗa. Idan kuma mutum yana jin haushin wani saboda Allah Ya ba shi wata ni’ima, yana kuma son ni’imar ta gushe daga gare shi, to wannan ita ce hassada wacce aka haramta.
Illon Mutum Ya Zama Maras Gibɗa:
Idan mutum bai da hali na gibɗa, to hakan zai haifar masa da:
• Rashin ƙwazo da son ci gaba a rayuwa.
• Rashin yin koyi da na-gari a al’umma.
• Watsi da neman ilimi da kwarewa a sana’a ko addini.
• Rashin gasa a ayyukan ibada, wanda zai iya sa mutum ya ja baya a addini.
Yadda Mutum Zai Zama Mai Gibɗa:
Idan mutjm yana son ya sami ta gari, to dole ne ya zamanto ya:
• Nemi arzƙi ta hanyar halal da nagartaccen ilimi mai amfani.
• Aiki tuƙuru don samun ci gaba, ba tare da cutar da wani ba.
• Yin addu’a don Allah Ya ba shi irin ni’ima da wasu ke da ita.
• Kauracewa hassada da kiyayya a zuciya.
Kallon wasu a matsayin abin koyi, ba makiya ba.
Allah Ya datar da mu. Amin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp