Farashin danyen man fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan da manyan kasashe masu arzikin man fetur suka bayyana rage adadin man da suke fitarwa.
Farashin ya karu da fiye da kashi biyar cikin dari, inda ya kai sama da Dala 84 a kan kowace ganga.
- Dubi Ga Sabbin Hanyoyin Kutse A Facebook, WhatsApp Da Asusun Ajiyar Banki
- Da ÆŠumi-É—uminsa: An Sa Dokar Hana Fita A Wasu Unguwannin Kaduna
Karuwar farashin na zuwa ne bayan kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC), suka ayyana cewa za su rage yawan man da suke fitarwa zuwa kasuwar da fiye da ganga miliyan daya a kowace rana.
Ko a watan Fabrairun bara ma, sai da farashin man ya tashi, bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
To sai dai sannu a hankali farashin ya ci gaba da sauka, inda har ya koma yadda yake kafin mamayar.
Masu sharhi na cewa karuwar farashin zai kawo cikas, a kokarin da duniya ke yi wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.