Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce farashin gas din girki mai nauyin kilo 5 ya karu zuwa N3,921.35 a watan Mayun 2022.
Wannan na kunshe ne a cikin wata kididdiga da NBD ta fitar kan farashin a watan Mayu 2022 da ta fitar a Abuja ranar Lahadi.
- Gwamnatin Zamfara Ta Bayar Da Hutun Kwana 5 Don Kowa Ya Samu Damar Zuwa Rijistar Zabe
- Majalisar Gudanarwar Sin Ta Nada Sabbin Jami’an Gwamnatin HKSAR
Hukumar ta NBS ta ce farashin ya karu daga N3,800.47 a watan Afrilun 2022, zuwa kashi 3.18 cikin 100 a wata daya.
A cewar NBS cikin shekara guda, matsakaicin farashin gas din girki ya karu da kashi 89.28 daga N2,071.69 a watan Mayu 2021.
Kididdigar ta nuna cewa an samu kari mafi girman a kan tukunyar gas mai nauyin kilogiram 5 a Gombe, wanda ake sayar da shi a kan N4,366.67, a Bayelsa kuwa ana sayar da shi a kan N4,325.00 sai Adamawa a kan N4,250.00.
A daya hannun kuma, ta ce a Yobe ana samun matsakaicin farashi na gas din a kan N3,200.00, sai Ogun sai Ondo ana samu a kan N3,450.00 da N3,480.77.
Rahoton ya ce farashin tunkuyar gas mai nauyin kilo 12.5 ya karu zuwa N8,726.30 a watan Mayu 2022 daga N8,164.37 a watan Afrilun 2022, wanda ke nuna karuwar kashi 6.88 a cikin wata daya.
NBS ta ce farashin na ci gaba da yin tafiyar hawainiya a jihohin daban-daban na kasar, inda kowace jiha aka samu karon farashin gas din na girki.