Manoman da ke yin noman rani a Dam din da ke Mashigi a kankara Kankara a cikin jihar Katsina, na samun dimbin kudaden shiga a fannin noman Rama har zuwa karshen shekara.
Daga shekarar 1960 zuwa 1970 har zuwa farkon 1980, ana shuka Rama ne don sarafa ta zuwa wasu nau’uka ciki har da Buhu.
A yau, mata da kuma yara da suka fito daga wasu garuruwa da kauyukan da ke a cikin jihar Katsina, na zuwa Dam din na Mashigi domin sayen Ganyen Rama don su dafa su kuma sayar wa masu bukata.
Shugaban masu kungiyar masu noman rrani Mallam Adamu Sani ya anar da cewa, monma a yankin sun dogara ne kan noman Rama, Albasa da kuma Dawa, sabanin a wasu yankunan da ake noman Tumatir, Dankalin hausa, Alkama da kuma Kabeji.
“Mata da kuma yara da suka fito daga wasu garuruwa da kauyukan da ke a cikin jihar Katsina, na zuwa Dam din na Mashigi domin sayen Ganyen Rama don su dafa su kuma sayar wa masu bukata.”
Ya sanar da cewa, sun kware a fannin noman Rama, Albasa da kuma Dawa, wasu ‘yan kadan daga cikin mu ke noma saran amfanin gona.
Sani ya ci gaba da cewa, idan bukatar Rama ya karu, ana sayar da danyar da Buhun Ganyenta daga Naira 3000 zuwa Naira 3500.
“Mun kware a fannin noman Rama, Albasa da kuma Dawa, wasu ‘yan kadan daga cikin mu ke noma saran amfanin gona.”
Shugaban ya kara da cewa, a kadada daya ana iya samun Buhu Buhu 10 a duk mako daya, musaman idan ana yiwa kadadar ban ruwan da ya dace da zuba takin zamani.
“A noman Rama na iya samun ribar Naira 35,000 daga kadada daya, inda ya sanar da cewa, mun fi son mu noma Rama fiye da Tumatir saboda kaucewa samun asara a noman na Tumatir.”
A cewarsa, a duk mako manoman Rama na iya samun ribar Naira 35,000 daga kadada daya, inda ya sanar da cewa, mun fi son mu noma Rama fiye da Tumatir saboda kaucewa samun asara a noman na Tumatir.
“A kadada daya ana iya samun Buhu Buhu 10 a duk mako daya, musaman idan ana yiwa kadadara ban ruwan da ya dace da zuba takin zamani.”
Shi ma wani manomin na Rama mai suna Abdullahi Lawal ya sanar da cewa, baya ga noman Rama ya na kuma noma Dawa mai yawa, inda ya sanar da cewa, noman Dawa na daya daga cikin hanyar samun kudaden shiga.
Lawal ya bayyana cewa, ana shuka Rama a watan Maris mu kuma girbeta a watan Mayu bayan ta bushe.
“Baya ga noman Rama ya na kuma noma Dawa mai yawa, inda ya sanar da cewa, noman Dawa na daya daga cikin hanyar samun kudaden shiga.”