A makon daya gabata ne hukumar kididdiga ta Nijeriya (NBS) ta sanar da rahoton cewa, kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin.
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya ce akwai sauran rina a kaba kafin hukumomin kasar su tabbatar da an kawo karshen matsalolin da suka addabi tattalin arzikin da yaki ci yaki cinyewa a kasar.
Ya bayyana wadannan kalaman ne a shafinsa na Twitter, inda ya fara da nuna farin cikinsa da samun labarin fitar kasar daga kangin tattalin arziki.
Atiku ya kara da cewa, “har sai lokacin da talakan Nijeriya zai iya cin abinci sau uku a rana ne za a ce koma bayan tattalin arziki ya kare”,inji shi.