Farfesa Haruna Musa ya samu nasarar zama wanda ya lashe zaben kujerar Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) bayan nasarar da ya samu a babban taron jami’ar. Farfesan ya samu ƙuri’u 853, ya doke sauran ‘yan takara a zaben da ya ja hankalin al’ummar jami’ar.
Jami’ar ta tabbatar da sakamakon zaben ta hannun shafinta na Facebook, inda ta bayyana nasarar Farfesa Musa a hukumance, alamar buɗe sabon babi a shugabancin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a Nijeriya.
- Jigawa Za Ta Samar Da Kashi 25 Na Shinkafar Da Nijeriya Ke Bukata – Hon Abdurahman
- Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149
Farfesa Musa, wanda ke matsayin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da harkokin karatu (Academics) a halin yanzu, ya fara karatunsa ne a makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Danbatta a shekarar 1985. Ya samu digiri na farko a fannin Chemistry daga BUK a 1991, sai digirin digirgir (Master’s) a fannin Polymer Chemistry a 1999, sannan ya kammala babban digirin digirgir (PhD) a fannin guda daga Jami’ar Bristol a Birtaniya a 2009.
A tsawon shekarun aikinsa, Farfesa Musa ya riƙe muhimman muƙamai a jami’ar, kamar Shugaban sashin Pure and Industrial Chemistry, Shugaban reshen ASUU na BUK, da kuma Mataimakin Darakta a Cibiyar Bunƙasa Makamashi da Sauyin Mai Ɗorewa (CREST). Ƙwarewarsa da jajircewarsa wajen inganta ilimi sun ba shi girmamawa daga abokan aiki da ɗalibai.
Sakamakon wannan zaɓe muhimmin ci gaba ne a tafiyar aikinsa, kuma yana nuna yarda da amincewar al’ummar jami’a da hangen nesansa. Ana sa ran jagorancinsa zai kai BUK mataki na gaba wajen ci gaban ilimi da kyakkyawan gudanarwa.














