Muhammad Maitela">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Fargabar Yaduwar Cutar Koda A Yobe!

by Muhammad Maitela
January 2, 2021
in RAHOTANNI
4 min read
Cutar Koda
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Jama’a da dama da ke arewacin jihar Yobe, su na ci gaba da bayyana fargar yadda gwamnatin jihar Yobe hadi da yan siyasar yankin ke ci gaba da jan kafa wajen gudanar da ingantaccen binciken da zai kai ga gano hakikanin abubuwan da ke jawo yawaitar kamuwa da cutar koda a yankin, matsalar da dadewa ta yi sanadiyyar mutuwar daruruwan jama’a, yayin da wasu da dama ke ci gaba da fama da matsalar.

 

samndaads

Har wala yau, wannan yanki shi ne shiyyar da shugaban majklisar dattawan tarayyar Nijeriya; Sanata Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ke wakilta, sama da shekara 20. Wanda a kan idon sa al’amarin ci gaba da lakume rayukan jama’ar da su ka zabe shi, ba tare da daukar kwakkwaran matakin da ya dace ba, face kawai daukar alkawurra. Sannaan wani babban abin damuwa, bai tabuka abin azo a gani ba wajen rage wa masu fama da cutar wahalhalun ta ba.

 

 

Binciken farko ya nuna yankin ne ya fi sauran yankunan jihar fama da lalurar cutar kodar, musamman kananan hukumomin Jakusko, Bade, Karasuwa da Nguru, a matsayin wadanda su ka fi kasancewa cikin barazanar wannan cutar, wadda har yanzu babu kwakkwaran binciken da ya tabbatar da hakikanin me ke haddasa matsalar ba.

 

Dukta Musa Abubakar, kwararren likita ne kana kuma shugaban asibitin gwamnatin tarayya (FMC) a Nguru da ke jihar Yobe, ya bayyana cewa mazauna arewacin jihar Yobe su ne ke kan gaba wajen barazanar kamuwa da cutar koda a arewa maso-gabas.

 

Dukta Musa ya kara da cewa, har yanzu bincike bai basu hakikanin inda matsalar take ba, abin ta ruwan sha ne ko a yanayin kasa ne ko wasu daga nau’in kayan abbincin da ake amfani da su a yankin, “Wannan al’amari ne mai matukar girma kuma wanda akwai bukatar gwamnatin jihar Yobe da tarayya su hada hannu wajen gudanar da kawakkwaran binciken yadda al’amarin yake tare da kokarin dakile shi. Sannan babbar matsalar ita ce yadda cutar ke ci gaba da shafar masu karamin karfi da matsakaita”.

 

 

A hannu guda kuma, wani binciken da cibiyar kula da masu fama da cutar koda ta asibitin koyarwar jami’ar Maiduguri (UMTH) ta gudanar a shekarun baya ya nuna yadda mafi yawan masu dauke da cutar a jihar, wadanda ke zuwa ganin likitoci a cibiyar, sun fito ne daga wannan yanki, a jihar Yobe.

 

Sakamakon binciken ya na kunshe ne a cikin wani rahoton da shugaban cibiyar ya jagoranta ya fitar- Farfesa Ibrahim Ummate, likitan tuntuba (consultant physician) kuma kwararren masani a fannin cutukan koda (nephrologis); na asibitin koyarwar jami’ar Maidugur (UMTH) a jihar Borno, wanda ya nuna cewa, majinyatan da dama ne daga yankin ke zuwa wankin koda a cibiyar. Ya ce kuma mafi yawan masu zuwa daga jihar sun fito ne daga wannan yankin.

 

Farfesa Ummate ya bayyana takaicin halin ko-in-kula da mahukuntan jihar Yobe tare da yan siyasar yankin ke nuna wa wajen jan-kafar gudanar da sahihin binciken abubuwan da ke da nasaba da faruwar matsalar cutar kodar. Ya ce har yanzu cibiyar bata gudanar da wani binciken kwakwab ba, wajen gano hakikanin abinda ke haifar da matsalar a yankin ba, ya ce su na kokari kan hakan.

 

Ya ce a kwarya-kwaryar binciken da su ka gudanar a shekarun baya- a matakin farko, sun yi kokarin fahimtar shin ko akwai matsalar hawan-jini tattare da al’ummar yankin, amma sai suka fahimci cewa babu.

 

Abu na biyu kuma, cutar koda bata daga cikin cutukan da mutanen yankin su ka gada iyaye da kakkani. Amma a karshe, sun yi hasashen cewa kila matsalar ta na da alaka da ruwan da jama’ar yankin ke amfani dasu a yankin. Binciken da wasu masana su ka yi watsi dashi.

 

Shugaban cibiyar, ya ce bisa ga hakan sun sha rubuta wasikun daukar matakan gaggawa zuwa ga gwamnatin jihar Yobe (Gwamna Gaidam), manyan yan siyasar yankin hadi da masarautar Bade, wajen neman cikakken goyon baya domin gudanar da binciken da zai kai ga gano hakikanin matsalar, ya ce amma shuru.

SendShareTweetShare
Previous Post

Matasa 60,000  Su Ka Yi Rajista Don Shiga Fannin Noma – Kwamishina

Next Post

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Ci Gaba Da Kaunar Juna

RelatedPosts

DATA

Har Yanzu Ana Sayar Da (DATA) Kan Tsohon Farashi Duk Da Ragin Kashi 50

by Muhammad Maitela
23 hours ago
0

Yawancin masu amfani da layin sadarwa sun ce har yanzu...

Farfesa Dadari

Yawan Karbo Bashin Da Gwamnati Ke Yi Bai Da Amfani Ga Kasar Nan -Farfesa Dadari

by Muhammad Maitela
23 hours ago
0

Wani Malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa...

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

Gobara Ta Yi Sanadiyyar  Mutuwar Uwa Da ‘Ya’yanta Biyu A Kirfi

by Muhammad Maitela
23 hours ago
0

Ibtila’in gobara ya ci rayuwar mutum uku daga ciki har...

Next Post
Shugaban Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Ci Gaba Da Kaunar Juna

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version