A shekarar 2007 aka fara yayata fasahar shuka shinkafa mai aure (wato hybrid rice a Turance) ta kasar Sin a Madagascar, don taimakawa kasar cimma burin tabbatar da wadatar abinci. Tun daga wancan lokacin, wani masanin kimiyya a bangaren shuka shinkafa na kasar Madagascar Mamisoa Ramananjanahary, ya fara yayata wannan fasahar Sin a kasarsa. Sau da dama Mamisoa ya samu kwasa-kwasai a kasar Sin, har makirkirin fasahar shinkafa mai aure ta kasar Sin, marigayi Yuan Longping, ya taba koya masa fasahar fuska da fuska.
Kwanan baya, lokacin da nake aikin daukar shirin “kwadon baka” a lardin Hunan da ke tsakiyar kasar Sin, mun samu shinkafar da Mamisoa ya aiko mana daga Madagascar wadda ya shuka, kuma ya bukace mu kai ta kabarin marigayi Yuan Longping don tunawa da shi, a matsayin mutumin da ya taimakawa kasar wajen tabbatar da wadatar abinci ta dogaro da kai.
- Ko Sabbin Dabarun Yaki Da Ta’adanci Za Su Yi Tasiri?
- An Cafke Wani Hedimasta Bisa Laifin Sayar Da Kayayyakin Makaranta A Kano
Ya zuwa yanzu, yawan shinkafa mai aure da aka shuka a Madagascar ya kai eka dubu 70, kana yawan hatsi da aka girba a ko wane eka ya kai ton 7, wani lokaci har ya kai ton 12, adadin da ya ninka har sau 2 bisa na nau’in irin shinkafar asalin wurin. Bisa bukatun kasar Madagascar a ko wace shekara, za a samar da isashen hatsi a kasar idan an kara shuka irin shinkafar Sin a gonaki masu fadin eka dubu 100. Domin tunawa da taimakon da Sin take baiwa kasar a bangaren shuka shinkafa mai aure, Madagascar ta kuma buga hoton shinkafa mai aure iri ta Sin a kan takardar kudinta.
Tabbatar da wadatar abinci aiki ne mai matukar muhimmanci ga ko wace kasa, kuma tushe ne na bunkasuwar tattalin arziki da kwanciyar hankalin al’umma. Kaza lika har kullum zamanintar da ayyukan gona wani muhimmin bangare ne na hadin gwiwar Sin da Afirka. A gun taron kolin FOCAC da ya gudana a kwanakin baya a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da manyan ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka guda 10, ciki har da samarwa kasashen Afirka tallafin hatsi da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 141 cikin gaggawa, da taimaka musu gina gonakin misali da fadinsu ya kai sama da eka dubu 6600, da ma tura masanan aikin noma 500 zuwa kasashen Afirka, har ma da kafa kawancen kirkire-kirkire fasahohin aikin noma tsakanin Sin da Afirka.
Mamisoa ya kama aikin shuka shinkafa mai aure ne sakamakon ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren aikin noma, mutane irinsu Mamisoa da ke dukufa a kan ayyukan gona bisa hadin gwiwar Sin da Afirka suna da yawa, wadanda suke kokarin neman tabbatar da wadatar abinci a kasashen Afirka, kana suke kokarin neman cimma burin zamanintar da kasashensu. (Mai zane da rubutu:MINA)