Wata fashewar gas ta haifar da gobara a unguwar Temidire da ke Reke, a ƙaramar hukumar Asa ta Jihar Kwara, inda ta lalata wani gida mai ɗakuna uku tare da asarar dukiya mai tarin yawa.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yammacin Lahadi, sakamakon malalar gas daga murhu, wadda ta haddasa fashewa kafin gobarar ta tashi.
- Shugaban Kasar Sin Ya Tattauna Da Takwaransa Na Faransa
- Tinubu Ya Umarci A Tsaurara Tsaro A Dazukan Kwara, Neja Da Kebbi
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa jami’an kashe gobara sun yi gaggawar kai ɗauki tare da daƙile yaɗuwar gobarar zuwa wasu gine-gine makwabta.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Prince Falade John Olumuyiwa, ya shawarci jama’a da su riƙa duba kayan amfani da gas akai-akai, su tabbatar da samun iska mai kyau, tare da kauce wa amfani da tukunyar gas da suka lalace domin kauce wa irin wannan haɗari.














