An yanke wa ’yan Nijeriya hudu da ke cikin wata kungiyar fashi ta wayoyi da ta addabi birnin Landan hukuncin daurin shekaru 55 gaba daya, a kotun Kingston Crown Court da ke Birtaniya.
Jaridar PUNCH Metro ta samo wannan bayanin ne daga wata sanarwa da aka wallafa a shafin Intanet UK Metropolitan Police a ranar Litinin.
- BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani
- Sin Ta Yi Tsokaci Kan Kalaman Da Firaministar Japan Takaichi Sanae Ta Yi A Kanta
A cewar sanarwar, wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Dabid Akintola, Ayomide Olaribiro, Olabiyi Obasa, da Dabid Okewole.
Sauran da ke cikin kungiyar sun hada da James Adodo, Robert Hills, Nelson Joel, Michael Babo, Mushtakim Miah, da Labille Bloise.
Sanarwar ta bayyana cewa tsakanin Satumba da Nuwamba 2024, kungiyar ta gudanar da akalla fashi 13 a shagunan waya daban-daban a fadin Birtaniya.
Ta ce, “Kungiyar ta fi kai hare-hare a shagunan EE, inda suke amfani da barazana da tashin hankali wajen tilasta ma’aikata su bude dakunan ajiya na sirri kafin su gudu da wayoyi masu tsada da sauran na’urori.”
A jimlace, sun sace kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan £240,000.
Jami’an tsaro sun gano masu laifin ta hanyar shaidar DNA, da kuma bayanan kira da rikodin motocin da suka yi amfani da su.
An ce sun ci gaba da bibiyar kungiyar yayin da take shirin sake kai wani hari, inda a ranar 19 ga Nuwamba, 2024, jami’ai suka yi musu kwanton bauna suka kama mutane hudu daga cikinsu a lokacin da suke kokarin yin fashi a wani shagon EE da ke Kilburn.
“Bincike a gidajen da ake danganta su da wadanda ake zargin ya kai ga gano kayan da aka sace da karin shaidu da ke hada kungiyar da fashi-fashin.”
Sanarwar ta bayyana cewa mutane 10 da aka kama a lokacin aikin an gurfanar da su a kotu, inda takwas suka amsa laifi na hadin gwiwa wajen fashi a ranar 30 ga Janairu.
Sanarwar ta kara da cewa bayan amsa laifin, an yanke musu hukuncin a ranar Jumma’a, 7 ga Nuwamba.
Ta bayyana tsawon lokacin da za su yi a gidan yari kamar haka:
James Adodo na St Martins Road, Dartford, Kent, an yanke masa hukuncin shekaru 10 a gidan yari.
Dabid Akintola na Samuel Street, Woolwich, an yanke masa hukuncin shekaru 6 da watanni 6 a gidan yari.
Michael Babo na Gilbert Close, Woolwich, an yanke masa hukuncin shekaru 6 da watanni 10 a gidan yari.
Robert Hills na Mayfield Road, Grabesend, Kent, an yanke masa hukuncin shekaru 5 da watanni 3 a gidan yari.
Ayomide Olaribiro na Warrior Skuare, Manor Park, an yanke masa hukuncin shekaru 4 da watanni 6 a gidan yari.
Nelson Joel na St Martins Road, Dartford, Kent, an yanke masa hukuncin shekaru 3 da watanni 3 a gidan yari.
Olabiyi Obasa na Norfolk Close, Dartford, Kent, an yanke masa hukuncin shekaru 3 da watanni 6 a gidan yari.
Dabid Okewole na Bale Road, Northfleet, Kent, an yanke masa hukuncin shekaru 7 da watanni 6 a gidan yari.
Sanarwar ta kuma nuna cewa wasu da aka yi kara biyu sun amsa laifin kokarin fashi, inda aka yanke musu hukuncin da ya dace.
Labille Bloise na Goldcrest Close, Thamesmead, an yanke masa hukuncin shekaru 2, wanda aka dage har tsawon shekaru 2.
Mushtakim Miah na Artillery Place, Woolwich, an yanke masa hukuncin shekaru 8 da watanni 6 a gidan yari.
Wannan shari’a ta zo ne a daidai lokacin da ake karuwa da rahotannin ’yan Nijeriya da ke kasashen waje da ake yanke musu hukuncin laifuka.
Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito a ranar Laraba da ta gabata cewa wani dalibi dan Nijeriya mai digiri na biyu da ke zaune a Birtaniya, Chiemka Okoronta, zai yi kaura daga kasar bayan ya yi zaman gidan yari na shekaru 10, saboda an same shi da laifin fyade kan wata yarinya.














