Abba Ibrahim Wada">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Fifa Ta Zabi Alkalan Wasanni Mata Uku Domin Alkalanci A Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada
January 6, 2021
in WASANNI
1 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta bayyana alkalan wasan da za su ja ragamar gasar Zakarun nahiyoyin duniya wato Club World Cup da za a yi a kasar Katar kuma an bayyana alkalan wasa bakwai da mataimaka 12 da za su gudanar da aikin har da masu kula da na’urar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato BAR.

Mata uku da aka zaba sun hada da Edin Albes Batista wadda ta hura wasa a gasar matasa ta duniya ta ‘yan kasa da shekara 17 a Indiya a 2017 da Esther Staubli da kuma Claudia Umpierrez, wadda ta alkalanci wasa biyu a gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 da aka yi a Brazil a 2019.

samndaads

A karshen makon nan ake sa ran dukkan alkalan da aka zabo za su kammala shirye-shiryen gabatar da kansu a Katar, kafin gasar ta kankama haka kuma kasar da za ta karbi bakunci da kuma Fifa za su gabatar da dukkan matakan kariyar yada cutar korona a lokacin gudanar da gasar da ya kamata a buga a badi, amma aka dage saboda bullar annobar.

Ranar 19 ga watan Janairu za a yi bikin raba jadawalin zakarun nahiyoyin da za su kara a tsakaninsu sannan za kuma a fara wasannin a Doha tsakanin 1 zuwa 11 ga watan Fabrairun 2021, inda ake sa ran buga wasan karshe ranar 11 ga watan Fabrairu.

SendShareTweetShare
Previous Post

’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum, Sun Yi Garkuwa Da 20 A Nasarawa

Next Post

Wajibi Ne Samar Da Wadataccen Abinci A Afirka – Masu Ruwa Da Tsaki

RelatedPosts

Klopp

Bai Kamata Mu Yi Rashin Nasara A Hannun Manchester Ba, Cewar Klopp

by Abba Ibrahim Wada
3 hours ago
0

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool,...

Arsenal

Har Yanzu Arsenal Tana Zuciyata – Ozil

by Abba Ibrahim Wada
5 hours ago
0

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa t arsenal, Mesut Ozil...

Za Mu Iya Samun Nasara Ba Tare Da Messi Ba – Koeman

by Abba Ibrahim Wada
6 hours ago
0

Duk da rashin Messi sakamakon horon dakatarwa na wasanni biyu...

Next Post
Abinci A Afirka

Wajibi Ne Samar Da Wadataccen Abinci A Afirka – Masu Ruwa Da Tsaki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version