Abdulrazaq Yahuza Jere" />

Filin Fatawa

Na Nemi Mijina A Kwanciyar Aure Bai Amsa Min Ba, Ko Yana Da Zunubi?

Tambaya:

Malam ina roko a taimaka min da amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matar sa don saduwa ita kuma ta ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijinta shi kuma yaki, shi ma ya aikata zunubi ne ko ko?

Amsa:

To dan’uwa hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa “Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ba ta amsa masa ba, to mala’iku za su tsine mata har ta wayi  gari”  kamar yadda Muslim ya rawito a hadisi mai lamba ta : 1436.

Saidai abin da malamai suke cewa shi ne : namiji ba shi da laifi,idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin namiji da mace sun bambanta, saboda mace za’a iya saduwa da ita ko da ba ta da sha’awa, namiji kuwa sai yana da sha’awa, zai iya saduwa, don haka akwai bukatar ace yana da nishadi kafin ya iya jima’i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin da za ta iya, sannan sha’awar maza ta fi ta mata karfi, saboda haka yawanci namiji ne  yake neman matarsa ba akasin haka ba.

Allah ne ma fi sani……

 

Fatawar Nan Akwai Gyara !

 

Malam fatawarka da ka yi akan mijin da matarsa ta neme shi da jima’i, bai amsa mata ba, ba shi da laifi, mun watsa ta a group da yawa, kuma ta hadu da kalubale, ga abin da wata take cewa:

Nake ganin idan har aka ce namiji kawai ne zai iya kusantar matarsa duk lokacin da ya so ko tana so ko ba ta so, ita mace idan ta nemi hakan ko bai biya ma ta bukatarta ba sai lokacin da ya so,Anya akwai adalci a hakan? Idan akwai istidlali nakli a taimakamin da su ba akali ba. Na ga istidlal din na akali aka kawo a rubutun.Ya za a yi mace ta nemi mijinta ya ki amince ma ta, duk da kasancewar mace tana da kunya. Amma har ta iya nemansa ka ga kuwa akwai dalilin da ya sa ta neme shi. Ai shi ma namiji ko da bai da sha’awa da an taba shi sha’awarshi za ta motsa.Kenan hakan ba zai zamo dalili da zai sa don mace ta nemi mijinta ba ya ki amincewa da dalilin wai baya da sha’awa.

Amsa:

To abin da zan iya cewa shi ne: saduwar da muke magana akanta ibada ce, ibada kuma tana bukatar dalili kafin a tabbatar da ita, babu wani dalili Wanda ya wajabtawa miji amsa kiran matarsa duk lokacin da ta neme shi, sannan yanayi da al’ada ya tabbatar da cewa namiji ba zai iya saduwa da mace ba duk lokacin da ta name shi, saboda Namiji yana bukatar nashadi kafin saduwa, sabanin mace, wacce take a matsayin katifa, wannan yasa malamai da yawa na sharia suka tafi akan cewa ba’a yiwa namiji fyade, tun da in azzakarinsa bai motsa ba, ba zai sadu da mace ba, mace kuwa an cimma daidaito za’a iya mata fyade saboda kamar tirmi take, in har an samu tabarya shike nan, wannan yasa za’a iya saduwa da mace tana bacci sabanin namiji.

Kasancewar an ce babu la’anta akansa idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba, ba ya nuna ya halatta ya cutar  da ita, yaki saduwa da ita a lokacin da yake da nishadi.

Allah ne mafi sani.

 

Zan Iya Auren Ma’aikacin Banki, Alhali Ina Tsoron Cin Haram?

 

Tambaya:

Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani ma’aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu’amalarsa za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari’a? Saboda tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.

Amsa:

To dan’uwa Annabi  s.a.w.  yana cewa : “Allah ya la’anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka” Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598.

Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu’amala da riba, saboda ma’aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike . .

Duba fatawaa Allajanah adda’imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.

Idan ya zama abin da ma’aikacin banki yake amsa haramun ne, kuma ba shi da wata sana’a sai wannan, akwai hadari a auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun

Malamai suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa,  saboda Annabi s.a.w. ya yi mu’amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata sana’a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa  ba.

Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.

Allah ne mafi sani.

Mijina Ba Ya Sallah, Ko Zan Iya Neman Ya Sake Ni?

Tambaya:

Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi? , na  gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam To ‘yar’uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi (SAW) ya fada a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81.

Ga shi kuma aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce.

Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta: 222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan.

Saidai zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.

Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.

Allah ne mafi sani

 

 

Ana Biyana Albashi, Amma Ba na Zuwa Wurin Aiki, Yaya Hukuncina?

Tambaya:

Assalamu Alaikum Warahmatullah? Barka da dare Dr dafatan kawuni lafiya Allah Yasa haka Shaikh Inada wata Tambayane a taimakamin da amsa. Dr, Matace tana aikin Gwamnati a wata jaha sai kuma barin Jahar ya kama su ita da mijinta ma’ana suka tashi kwata-kwata daga Wannan Jahar sai ya zama bata zuwa aikinta amma kuma Ana bata Salary duk wata amma Principal din makarantar da take aiki yana sane shi ya amince mata ta tafi sai kuma wani Ma’aikacin ma’aikatar Ilmi to amma ma’aikatar ba ta da masaniya, to Dr. Yaya kudin da take karba duk wata ya halatta ta ci gaba da karba ko ta daina karba? don Abin yana damunta tana ta tunanin abun koda yaushe. A taimaka min da Amsa Dr. Bissalaam.

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Bai halatta ta ci ba, saboda albashi ana bayar da shi ne ga wanda ya yi aiki, halattawar da principal ya yi mata ba zai ba ta damar cin kudin ba tun da ba mallakarsa ba ne, kudin al’uma ne mabukata.

Hukuncin yana zagayawa ne tare da sanuwar dalilinsa ko rashinsa.

Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi a rai, kuma ka ji tsoran kar mutane su tsinkayo kai, kamar yadda hadisi ya tabbatar.

Allah ne mafi sani

 

Hallacin Addu’a Da Hausa A Sujjada!!

Tambaya:

Assalamu alaikum. Akramakallahu mutum zai iya yin adduar neman wani abu a sujudar sallar farilla da wani yare koma bayan larabci?

 

Amsa:

To dan’uwa Annabi (SAW) yana cewa: “Amma sujjada to ku dage da addu’a saboda ya kusa a amsa muku” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 479,

Malamai sun yi sabani akan yin addu’a a sujjada da yaran da ba larabci ba, amma zance mafi inganci shi ne halaccin yin addu’ar da take ta neman wani abu a wajan Allah da yaran da ba larabci ba ga wanda bai iya larabci ba, saboda Allah ba ya kallafawa rai sai abin da za ta iya, sannan kuma Allah yana gane duk yaren da mutum ya yi addu’a da shi, amma wasu malaman sun karhanta yin zikirorin da suka zo a hadisi da yaran da ba larabci, saboda Annabi (SAW) ya fade su ne don su zama ibada, wannan yasa ba za’a canza su da wasu lafuzan ba.

Allah ne mafi sani.

Duba: Muhallah na Ibnu hazm 4\159 da Majmu’ul fataawa na Ibnu-taimiyya 22\488.

…………………………………………………………………………….

Page 27

Mace Za Ta Iya Yin Fitsari A Tsaye?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Don Allah malam mene hukuncin yin fitsari a tsaye ga mace ko namiji a Musulunci?

 

Amsa:

Ya halatta ga namiji ya yi fitsari a tsaye, saboda hadisin da Bukhari ya rawaito cewa: “Annabi (SAW) ya je jujin wasu mutane sai ya yı fitsari a tsaye”kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi na 222…

Tare da cewa duk hukuncin da ya zo dağa Annabi (SAW) yana hada mace da namiji, in ba’a samu abin da ya kebance shi ba, Tabbas fitsarin mace a tsaye zai jawo matsala wajan cikar tsarkinta, saboda yanayin halittar da Allah ya yı mata.

Yana daga cikin Ka’idojin sharia gabatar da wajibi akan abin da aka halatta, yin fitsari a tsaye ya halatta ga mace, saidai zai kai ga kunci wajan tabbatar da Dhahara, wacce sallah ba ta ingantuwa saida ita.

Duk hadisan da suka zo cewa Annabi ya hana yin fitsari a tsaye ba su inganta ba, sai hadisin Nana A’isha wanda Hakim ya inganta, in da take cewa: “Duk wanda ya ce muku Annabi (SAW) ya yi fitsari a tsaye kar ku gaskata shi” kamar yadda Nasa’i ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 29.

Malamai suna cewa: za’a dau maganarta akan tana bada labari ne, akan abin da ta gani, wannan ba ya kore a samu wani abin daban wanda ba ta sani ba, tun da ba koyaushe take zama tare da shi ba, yana daga cikin Ka’idoji a wajan malaman Usulul-fikhi:

Duk wanda ya tabbatar da abu za’a gabatar da maganarsa akan wanda ya kore, saboda wanda ya tabbatar yana da Karin ilimi na musamman wanda ya buya ga wanda ya kore.

Don neman Karin bayani duba: Sharhu Assuyudy ala Sunani Annasa’I 1\26.

Allah ne mafi sani.

 

Mene Ne Hukuncin Yin Gulmar Shugabanni Da ‘Yan Siyasa?

Tambaya:

Assalamu Alaykum, Yaa Shaykh, menene hukuncin magana akan shugabanni da ‘yan siyasa?  Shi ma gulma ne ko akwai bambanci idan mutumin yana da nauyin yiwa al’umma shugabanci da hidima?  Jazakumullahu Khayran…

 

Amsa:

Wa’alaykumussalam, To dan’uwa Allah da manzonsa sun haramta cin naman mutane, sannan malamai suna cewa: gulmar shuwagabanni da malamai ta fi tsananin haramci, saboda cin naman shuwagabanni zai jawo ayi musu tarzoma, kamar yadda cin naman malami zai jawo a raina ilimi, saidai akwai wuraren da ya halatta a ci naman mutane saboda maslaha, kamar idan aka zalunci mutum to ya halatta idan zai kai kara ya bayyana zaluncin da aka yi masa, haka nan idan ya ga wani sharri yana so a taimaka masa wajan gusar da shi to ya halatta ya fadi sunan mai laifin, kamar yadda kuma ya hallata ayi gulmar mutumin da ya shahara da aikata sabo da fasikanci, don a guji sharrinsa. Duba Azkar: 489 da kuma Majmu’ul fataawa 28\221.

A bisa abin da ya gabata za mu fahimci cewa: duk kasar da ake kafa shugaba ta hanyar zabe, to ya hallata mutane su tattauna matsalolin shugaban da yake kai, domin tunanin kawo canji a zabe mai zuwa, musamman idan shugaban ya kasance azzalumi kuma fasiki mai yawan aikata sabo, saidai ya wajaba maganar ta su ta zama gwargwadon bukata.

Allah ne mafi sani.

 

Mijina Yana Chatting Da Tsohuwar Buduwarsa Bayan Ta Yi Aure, Me Ya Kamata Na Yi?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum. Allah ya taimaki Dr, mijina ne suke chat da wata matar aure, wadda tsohuwar budurwarsa ce a baya sama da shekara 20 da wani abu ta yi aure, suna turawa juna hotuna, shin malam wata shawara da nasiha ya kamata na yi masa Sabo da kubutar da su ga fada wa halaka? Allah ya taimaki mallam ya kara fahimta.

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Ki yi masa nasiha da tsoran Allah, sannan kuma ki nuna masa cewa: Inda matarsa ce ba zai so ayi irin wannan mua’malar da ita ba.

Yin chatting irin wannan da matar aure yana iya kaiwa zuwa zina, musamman da alama har yanzu kuna son juna, Allah ya hana duk abin da zai kusantar zuwa Zina a suratul Isra’a’i.

Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai. Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye Shi, wanda ya saba masa zai hadu da Shi a madakata.

Dayanku ba zai yi cikakken imani ba har sai ya sowa dan’uwansa abin da yake soma kansa.

Allah ne mafi sani.

 

 

Na Saki Matata Sau Biyu, Sai Na Sake Sakinta Bayan Daura Sabon Aure, Ko Akwai Damar Kome?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai na ji daga gareka…

 

Amsa:

To dan’uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in  ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu .

Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta, da ba’a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani  ba, ya wajaba ku hakurewa juna .

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 7\388 .

Allah ne mafi sani.

 

 

Idan Kwarto Ya Danganta Wa Kansa Dan Zina Zai Iya Cin Gadonsa?

 

Tambaya:

Asslamu alaikumm. Dr. da Allah amin bayani akan dan zina, wanda an san hakikanin wanda ya yi cikin. shin zai ci gado?, za a iya ambatarsa da sunan wanda yayi cikin?,

Amsa:

To dan’uwa malamai sun yi sabani akan wannan mas’alar zuwa maganganu guda biyu:

  1. Maganar mafi yawan malamai ita ce: dan zina ba’a danganta shi zuwa kwarto, don haka ba zai ci gadonsa ba, saboda fadin Annabi (SAW) “Da na mai shimfida ne, shi kuma kwarto ba shi da hakki” kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 6368.
  2. Idan har matar ba ta da aure kuma wanda ya yi zinar ya danganta dan da aka samu ta wannan hanyar zuwa gare shi, kuma ba wanda ya ja da shi akan haka, to ya halatta a danganta masa dan, masu wannan maganar sun kafa hujja da cewa: hukuncin da Annabi (SAW) ya yi na cewa: Yaro ana danganta shi ne ga mai shimfida, yana kasancewa ne ga matar aure, amma wacce ba ta da aure, idan ta yi zina, kuma kwarto ya ce ya ji ya gani, za’a iya danganta shi zuwa gare shi, Wannan shi ne ra’ayin Urwa da Ibnu Siiriin da Ishak dan Rahuya da Ibnul-kayyim.

Wannan yana nuna cewa duk matar da take da miji, idan aka yi zina da ita, to za’a dangantawa mijinta abin da aka samu, saboda hadisin da ya gabata, amma matar da ba ta da miji, to kwartonta zai iya danganta dan aka samu zuwa gare shi a maganar wasu malaman, in har ya danganta kuma, to zai dauki dukkan hukunce-hukuncen da ake bawa cikakken Da.

Allah ne mafi sani.

Don neman Karin bayani duba: Zadul-ma’ad 5\374.

 

 

Alamomin Karbar Tuba

 

Tambaya:

Assalamu alaikum dan Allah malam akwai hanyar da mutum yake gane Allah ya yafe masa zunubin da ya yi, ya kuma nemi yafiya?

 

Amsa:

To dan’uwa akwai alamomin da malamai suka fada, wadanda suke nuna Allah ya karbi tuban bawansa, ga wasu daga ciki :

  1. Aikata ayyukan alkairi, da son yin abin da zai kusantar da shi zuwa ga Allah.
  2. Mutum ya dinga kallon gazawarsa wajan biyayya ga Allah.
  3. Ya zama yana yawan girmama zunubin da ya tuba daga shi, yana kuma jin tsoron komawa zuwa gare shi .
  4. Ya dinga kallon dacewar da aka ba shi ta tuba, a matsayin ni’ima daga Allah.
  5. Ya zama yana yawan nisantar zunubai, sama da kafin ya tuba.
  6. Yawan istigfari.
  7. Son kusantar salihan bayi.

Allah ne ma fi sani.

Exit mobile version