Sabon firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana da cikakken kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar. Yana mai cewa, za ta magance abubuwan dake neman hana ruwa gudu, don samun kyakkyawar makoma.
Li Qiang ya shaidawa taron manema labarai hakan ne Litinin din nan, bayan kammala taron farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14.
Li ya ce, idan har ana fatan cimma burin samun bunkasuwar yawan GDP da ya kai kusan kashi 5 bisa 100 a shekarar 2023, bisa babban tushen da ake samu a fannin tattalin arzikin kasar a halin yanzu, to hakan ba abu ne mai sauki ba, kuma yana bukatar kara zage damtse.
Ya kara da cewa, babban makasudin aikin jam’iyyar da ma gwamnati shi ne, kyautata jin dadin jama’a. Don haka wajibi ne a ko da yaushe gwamnati ta yi shiri tare da gudanar da ayyukanta bisa laakari da abin da jamaa ke ji da kuma aiwatar da bukatun jamaa.
Li Qiang ya bayyana cewa, kamfanoni masu zaman kansu dake kasar Sin, za su more yanayi mai kyau da kuma babbar dama ta samun ci gaba.
Li ya fadawa taron manema labarai cewa, gwamnati za ta kara zage damtse wajen samar da yanayin kasuwanci mai dogaro da kasuwa, bisa tsarin doka da kuma kasa da kasa, da kula da dukkan nauoin kamfanoni ba tare da nuna wani bambanci ba, da kare yancin mallakar kamfanoni da hakkoki da muradun yan kasuwa bisa doka.
Li ya bayyana cewa, kasar Sin za ta samar da daidaito ga kowane nau’in kasuwanci, da kara tallafawa kamfanoni masu zaman kansu, wajen bunkasa harkokinsu na kasuwanci.
Li Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara fadada bude kofa ga kasashen waje bisa manyan ka’idojin cinikayya na kasa da kasa, kuma za ta kara bude kofarta ga duniya tare da kyautata yanayin kasuwanci da samar da hidimomi.
Da yake karin hakse game da dangantakar Sin da Amurka kuwa, Li ya ce, Sin da Amurka za su iya yin hadin gwiwa, kuma dole ne su yi aiki tare, akwai kuma abubuwa da dama da kasashen biyu za su cimma ta hanyar yin aiki tare.
Li ya kara da cewa, matsayar da aka cimma tsakanin manyan shugabannin kasashen Sin da Amurka a yayin ganawar da suka yi a watan Nuwamban da ya gabata, na bukatar a fassara ko aiwatar da su zuwa hakikanin manufofi da ayyuka na zahiri. (Ibrahim Yaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp