Fitaccen mai watsa shirye-shiryen talabijin da rediyo, Larry King, wanda yake hira da duk wanda ya cancanci a yi hira da shi ko sanannan mutum a duniya, King ya shafe shekaru sittin akan wannan matsayin, ya mutu ranar Asabar yana da shekara 87.
Kamfanin da ya kafa, Ora Media, bai bayyana abin da ya yi sanadiyar mutuwarsa ba amma rahotannin kafofin yada labarai sun ce King ya kwashe makonni yana fama da cutar korona kuma ya sha fama da matsalolin rashin lafiya da dama a shekarun baya.
“Tsawon shekaru 63, yayi shirye-shirye da yawa a fannin gidan rediyo, telebijin da kafofin watsa labarai na zamani (intanet), ya samu kyaututtuka, da karramawa ta duniya a matsayin wata shaida ce ta kwarewarsa ta musamman a matsayin mai watsa labarai,” in ji Ora Media a cikin wata sanarwa da ta rubuta Twitter.