• English
  • Business News
Wednesday, October 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fitiyanul Islam Za Ta Kaddamar Da Asusun Taimaka Wa Marayu Ranar Alhamis Mai Zuwa

by Sulaiman
3 years ago
Fitiyanul Islam

Ƙungiyar addinin Musulunci ta Fitiyanul Islam ta Nijeriya ta bayyana cewa za ta samar wa dubban marayun da hare-haren ta’addanci su ka raba su da iyayen su a faɗin ƙasar nan matsuguni.

Ƙungiyar ta ce saboda haka ne ma za ta ƙaddamar da wani asusu na musamman a ranar Alhamis mai zuwa, 15 ga Disamba, 2022 domin gina Gidan Marayu na Sheikh Ibrahim Inyass da Cibiyar Koyar da Sana’o’i a Zariya cikin Jihar Kaduna.

  • Rundunar Soji Sun Kashe Mayakan Boko Haram 6 A Borno

A sanarwar da ya rattaba wa hannu, Mataimakin Sakatare Janar na ƙungiyar, wanda kuma shi ne Shugaban babban kwamitin shirya taron na ƙasa, Dakta Musa Muhammad Imam, ya ce za a yi ƙaddamarwar ne a lokacin babban taron ƙungiyar na shekara-shekara wanda za a gudanar a ɗakin taro na Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da ke Maitama, Abuja.

Ya ce haka kuma za a gudanar da zaɓen shugabannin ƙungiyar na ƙasa a washegarin ranar taron.

Dakta Imam ya ce babban baƙo na musamman shi ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yayin da shugaban taron shi ne mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Fitiyanul Islam

Mataimakin babban sakataren ya ce babban mai ƙaddamarwa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sannan babban baƙo mai jawabi shi ne Babban Limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari.

Ya ƙara da cewa uban taron shi ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, yayin da iyayen taro su ne Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da Sheikh Shariff Ibrahim Saleh.

Sanarwar ta ce babban mai masaukin baƙi shi ne Ministan Gundumar Birnin Tarayya, Alhaji Muhammad Musa Bello, yayin da Sanata Abu Ibrahim da ɗan takarar gwamna na APC a Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, za su kasance masu taimaka masa.

Dakta Imam ya yi fatan ɗaukacin Musulmi za su yi ƙoƙari su halarci taron domin fa’idar sa.

Ita da ƙungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya (FIN), an kafa ta ne a cikin 1962 a Kano a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Inyass Al-Kaulahi (rta), kuma tun daga lokacin ta kasance mai taka muhimmiyar rawa wajen da’awar addinin Musulunci ta hanyar ɗaruruwan makarantun ta da ke cikin Nijeriya da sauran ƙasashen yankin Afrika ta Yamma.

Haka kuma ta kan yi aikin yaɗa koyarwar Annabi Muhammadu (s.a.w.), wanda ya haɗa da zaman lafiya da juna, da tsare dokokin addini da kuma neman ilimin addinin Islama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Qatar 2022: Buhari Ya Jinjina Wa Morocco Kan Daukaka Darajar Afirka

Qatar 2022: Buhari Ya Jinjina Wa Morocco Kan Daukaka Darajar Afirka

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja

Majalisa Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kai Agajin Gaggawa Ga Waɗanda Fashewar Tanka Ta Shafa A Neja

October 22, 2025
Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar

October 22, 2025
Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki 

October 22, 2025
Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

Ba A Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla A Arewacin Nijeriya – Sarkin Musulmi

October 22, 2025
Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025 Na Jaridar Leadership: Dauda Lawal

October 22, 2025
Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

Shugaban NAHCON Ya Musanta Zargin Tsare Ɗan Jarida Da Aikata Cin Hanci

October 22, 2025
Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars

October 22, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

October 22, 2025
ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta

October 22, 2025
Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

Rashin Abinci Mai Gina Jiki Barazana Ce Ga Lafiyar Al’umma – Gwamna Lawal

October 22, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.