Za a kaddamar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) a birnin Beijing na kasar Sin a ranar 4 ga wata mai zuwa, inda dimbin shugabannin kasashe daban daban na nahiyar Afirka, ciki har da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, za su halarci taron. Watakila za ka so tambaya kan cewar me ya sa dimbin kasashen dake nahiyar Afirka ke dora matukar muhimmanci kan taron?
Don samun amsa ga tambayar, za a iya duba makalar da Charles Onunaiju, darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta Najeriya, ya rubuta, wadda aka wallafa a shafin yanar gizo ko Internet ta jaridar The Punch ta Najeriya, a ranar 26 ga watan da muke ciki. Cikin makalar, Mista Onunaiju ya ce, tsarin FOCAC ya riga ya zama wani dandalin hadin kan kasa da kasa mafi tasiri a nahiyar Afirka, wanda ya samar da dimbin ayyukan da suke taimakawa kokarin horar da ma’aikata a nahiyar Afirka, da biyan bukatun jama’ar nahiyar na kyautata zaman rayuwa, da sassanta yanayin da ake ciki na karancin kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afirka.
- Tawagar Jiragen Rundunar Sojin Saman Kasar Sin Ta Tafi Masar Domin Halartar Wani Bikin Nune-Nune
- Inganta Raya Shawarar BRI Zai Zama Daya Daga Manyan Batutuwan Da Za A Tattauna A Gun Taron Kolin FOCAC Na Bana
A cewar Mista Onunaiju, tarukan kolin FOCAC guda 2 da suka gabata sun sa kasashen Afirka samun rancen kudi da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 120, don biyan bukatunsu na raya wasu muhimman bangarori na hadin gwiwa, da suka shafi raya kayayyakin more rayuwa, da masana’antu, da zamanantar da aikin gona, da dai sauransu. Ta wannan hanya aka sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin kasashen Afirka, da haifar da dimbin guraben aikin yi, da habaka cinikin da ake yi tsakanin kasashe daban daban dake nahiyar Afirka. Mista Onunaiju ya kuma takaita ra’ayinsa kamar haka: “Dandalin tattaunawar FOCAC bai tsaya kan kasancewar wani dandali na tattaunawa da musayar ra’ayi kawai ba. Shi ma ya haifar da dimbin sakamako masu amfani, da tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasashen Afirka”.
Hakika Mista Onunaiju ya bayyana dalilin da ya sa kasashen Afirka ke dora muhimmanci kan taron FOCAC, wato saboda FOCAC din ba wani dandalin tattaunawa kawai ba ne, maimakon haka, ya kasance wani tsarin hadin gwiwa na aiwatar da matakai, da cika alkawari, don haifar wa kasashen Afirka da damar samun hakikanin ci gaba.
To, ta yaya ake kokarin cika alkawari? Kasar Sin ta sanar da manyan ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka guda 9, a taron ministoci karon 8 na dandalin tattaunawar FOCAC na shekarar 2021. Zuwa yanzu, an aiwatar da ayyukan yadda ake bukata, tare da samar da dimbin nasarori. Idan mun dauki aikin rage talauci da tallafawa manoma a matsayin misali, kasar Sin ta aiwatar da ayyuka 47 na rage talauci, da hadin gwiwa a fannin aikin gona, a kasashen Afirka, tare da horar da manoma kimanin dubu 9, da yayata fasahohin zamani fiye da 300, inda aka haifar da alfanu ga iyalai na manoma fiye da miliyan 1 dake nahiyar Afirka. Ban da haka, fasahar noman laimar kwado ta kasar Sin da ake kira fasahar Juncao ta sa mutanen Afirka fiye da dubu 100 samun karin kudin shiga, yayin da fasahar noman shinkafar zamani da aka tagwaita mai samar da yawan iri ko Hybrid ta kasar Sin, ta ba da damar kara yawan shinkafar da ake samu a kasashen Afirka daga ton 2 zuwa ton 7.5 kan kadada guda.
Yadda kasar Sin ke cika alkawari shi ma ya shafi yadda kasar ke amsa kiran da kasashen Afirka suka yi mata, don tabbatar da amfanin juna, da samun moriya tare, a hadin gwiwar da ake yi tsakaninsu. Misali, bayan da kasashen Afirka suka gabatar da korafe-korafe kan batun rashin daidaito a cinikayyar da ake yi tsakanin Sin da Afirka, kasar Sin ta fara daukar matakin sa kaimi ga aikin shigar da kayayyaki daga kasashen Afirka. Inda ta yafe ma kasashe marasa karfin tattalin arziki 21 dake nahiyar Afirka harajin kwastam bisa kaso 98% na kayayyakin da suke sayarwa a kasuwannin Sin, haka kuma an bude hanya mai sauki da ake kira “Green Lane” ga aikin shigar da amfanin gonan kasashen Afirka cikin kasar Sin. Haka zalika, kasar Sin ta ba kasashen Afirka damar sayar da karin amfanin gona a kasuwannin Sin ta hanyar kasuwanci ta yanyar gizo ko Internet. Wadannan matakan da aka dauka sun sa yawan amfanin gonan kasashen Afirka da aka sayar zuwa kasar Sin karuwa cikin shekaru 7 a jere. A shekarar 2023, nau’o’in gyada da kasar Sin ta shigar da su daga kasashen Afirka sun karu da kaso 130% bisa makamancin lokacin shekarar 2022, yayin da kayayyakin lambun da kasar ta shigar daga Afirka sun karu da kaso 32%. Ban da haka, a rabin farko na shekarar bana, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 60.1, wadda ta karu da kaso 14% bisa makamancin lokacin bara.
Mista Onunaiju ya rubuta a cikin makalarsa cewa, “Wata shaharariyar halayyar kasar Sin ita ce: Nacewa ga shirin da aka tsara, gami da kokarin aiwatar da shi. Wadda ta kasance wani babban dalilin da ya tabbatar da tasowar tattalin arzikin kasar. ” A zahiri dai, wannan halayya ita ma ta zama tushen karfafawar hadin gwiwar Sin da Afirka a kai a kai. (Bello Wang)