Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-Ma a Jihar Katsina (FUDMA), za ta karrama sakarakunan Bichi da Daura da kuma tsohon Gwamnan Jihar Katsina da digirin girmamawa a ranar Asarar.
Kamar yadda mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Armaya’u Bichi, ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewa jami’ar za ta karrama mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero, da mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar da kuma tsohon Gwamnan jih6ar Katsina Barista Ibrahim Shema.
- Zaben Kano: Alkali Na Fuskantar Tuhuma Kan Kuskuren Da Aka Tafka
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Maraba Da Shigowar Masu Zuba Jari Daga Mexico
Farfesa Armaya’u Bichi, ya kara da cewa a lokacin bikin yaye daliban jami’ar karo na biyu, za a gudanar da lakca wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Natsu Jinin Maliya zai gabatar.
Haka kuma ya kara da cewa akwai liyafar cin abinci ta dare da aka shirya domin karrama shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsin-Ma duk a cikin shirye-shiryen wannan biki mai cike da tarihi.
Mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsin-Ma, Farfesa Armaya’u Bichi, ya ce za su yaye daliban 4,364, inda ya ce mutum 112 za su fita da digiri mai daraja ta daya (first class) sai mutum 1,131, za su fita da digiri mai daraja ta biyu babba (second class upper) sai mutum 2,476 za su fita da digiri mai daraja ta biyu ( second class lower) karrama sai kuma mutum 646 za su fita da digiri mai daraja ta uku (third class).
“A karon farko za mu yaye daliban 401da suka hada da mutum 11 masu digirin digirgir (PHD) sai 168 masu digiri na biyu a fannin Ilimi (Acadamic masters) sai kuma mutum 75 masu digiri na biyu a fannin kwarewa (Professional Masters) tare da mutum 149 masu babar difloma duk lokacin baban taron yaye daliban na wannan shekarar,” in ji shi
Haka kuma ya bada tabbacin da irin shirin da suka yi na kammala wannan taro lafiya duk da irin barazanar tsaron da ake fuskanta a wannan gari na Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina.