Mukaddashin kwantirulan janar na hukumar kula da gidajen gyaran tarbiyya (NCoS), Sylbester Nwakuche, ya shaida cewar fursunoni 48,932 a halin yanzu da suke tsare a gidajen hari da suke sassan kasar nan na zaman jiran shari’a.
Nwakuche ya shaida hakan yayin da ke ganawa da jami’ansa a ranar Litinin, ya lura kan cewa cunkoson fursunoni da ake fama da su a gidajen gyaran tarbiyya a fadin kasar nan akwai bukatar a gyara su.
- Sinawa Kimanin Miliyan 1.85 Za Su Rika Zuwa Yawon Bude Ido a Ketare Kullum Lokacin Hutun Bikin Bazara
- INEC Ta Goge Sunayen Matattu 7,746 Daga Rajistar Zabe
Ya sanar da cewa hukumar za ta yi aikin hadin guiwa da Antoni Janar na kasa, shugaban ‘yansanda na kasa da sauran hukumomin gurfanar da masu laifi don hanzarin yin Shari’un fursunonin da ke zaman jiran shari’a.
Nwakuche ya ce akwai shirin da ake da shi na rage kwararowar dauraro domin tsaftace gidajen gyaran tarbiyya da suke fadin kasar nan.
Ya bukaci jami’an da ke kai fursunoni kotuna da su yi hadin guiwa jami’an jihohi, ciki har da manyan alkalai, kwamishinonin shari’a domin inganta harkokin shari’a da sauran yanke hukunci.