Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya zargi ‘yan siyasa waje haddasa rikice-rikice a lokacin zabe.
Ganduje ya bayyana wannan zargi ne a lokacin da tawagar jami’an hukumar zabe ta kasa (INEC) suka ziyarce shi a shalkwatan jam’iyyar APC da ke Abuja.
Ya ce, “Na san cewa babbar matsalar hukumar INEC shi ne, gudanar da zabe cikin tashin hankali. Kowa yana dora laifin kan INEC, amma kuma ‘yan siyasa ne ke dagula lamuran.
“Domin sanin dokokin zabe wajen tsaftace siyasa, dole ne cibiyoyinmu su fadakar da mutanenmu a lokaci bayan lokaci domin sanin dokokin zabe tare da sabunta su a zamanance. Hakan ba zai taba yuwuba sai an samu hadin kan ‘yan siyasa.”
Ganduje ya yaba wa jami’an hukumar INEC bisa gudanar da wannan ziyara, inda ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da ilmantar da mutane a wannan shekara har zuwa lokacin da za a gudanar da zabe mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar APC ya ce, “Mun bayar da umurni ga dukkanin jami’anmu da ke gundumomi da kananan hukumomi da na jihohi su kasance ofishominmu suna aiki domin mu samu damar gudanar da wannan lamari na fadakar da jama’a.”