A duk ranar 26, na watan Janairun kowacce shekara ne, ake gudanar da bikin zagayowar ranar tunawa da masu larurar cutar Kuturta.
Nijeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya, wajen gudanar da bikin zagayowar ranar, tunawa da masu larurar Kuturta, ta wannan shekarar.
Mahimmancin wannan ranar ita ce, gano cutar a kan lokaci da kuma yadda za a magance ta.
Take taron na wannan shekarar 2025 shi ne, “Hada Kai, Domin Kakkave Cutar, wadda ke da mahimmanci a kawo karshen ta, fadin duniya”.
Manufar ita ce, domin a wayar da kai kan cutar, bayyana kalubalen da masu larurar ke fuskanta, tare da hada kai, domin a dakile cutar.
- Karon Farko A Shekarar 2025: Turken Rarraba Hasken Wutar Lantarki Ya Fadi A Nijeriya
- ‘Yan Nijeriya Ku Kauracewa Amfani Da Layukan Waya Na MTN, Airtel Da Glo – NLC
Muna sane da cewa, cutar a yanzu, ta kai akalla shekaru 4,000, inda hakan ya sanya ta kasance daya daga cikin tsoffin cutukan da alumma suka san da su,
Hukumar jin kai ta kasar Faransa wato Raoul Follereau ce, ta zavo wannan ranar, domin girmama rayuwar marigayi Mahatma Gandhi, da ya mutu a watan Janairun 1948.
Gandhi, a lokacin yana raye, ya yi aiki tukuru, domin tallafawa masu larurar.
Kimanin mutane 200,000 da suka kamu da cutar ne, ake duba lafiyarsu ako wacce shekara a kasashe 120, inda kuma wasu da dama, ke ci gaba da rayuwa da wasu nau’ukan cutar, musamman a yankin Asiya, Afrika da kuma a Kudancin Amurka.
Kazalika, cutar ta kasance, ta na daga cikin cututtukan da aka yi watsi da batunsu a yankin nahiyar Afirka wadda kuma ta ci gaba da zama abin damuwa, ga vangaren kiwon lafiya a kasar nan.
Sai dai, za a iya cewa, Nijeriya ta samu nasara a shirinta na kasa, na yakar cutar kusan kasa da yawan alummarta daya a cikin dubu goma a shekarar 1998.
Duk da wannan nasarar ta Nijeriya ta samu, akwai batutuwan maganar al’ada, kin sauya dabi’a da har yanzu, ke ci gaba da janyo samun vullar cutar a kasar.
Idan za a iya tunawa, Shirin Dakile Yaduwar Cutar Fuka da Kuturta ta kasa NTBLCP, da aka faro shirin a shekarar 1989, daga shekarar 1991 zuwa shekarar 2012, kimanin masu larurra su 111,788 aka bai wa magunguna masu karfi domin duba lafiyarsu
Kazalika, Nijeriya ta kuma samun wani tallafi daga Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO na dakile cutar wanda ya kai kasa da duba lafiyar masu larurar su 10,000 a shekarar 2000.
Bisa saurin gano cutar a kasar nan, hakan ya sanya an samu kasa da kashi biyar, a cikin duk mutane 10,000, wanda hakan ya sanya a yanzu a Nijeriya aka samu raguwar cutar.
Sai dai, a wani matakin akwai yankunan da cutar ke yin kamari, inda ta kai ga a cikin duk mutune 10,000 ake samun mutum daya, na dauke da cutar.
Bugu da kari, kashi 10 aka samu na cutar a fadin Afirka a 2019, wanda a Nijeriya, da wasu kasashe 12 aka ruwaito cewa, an samu vullar cutar da ta kai daga 1,000–10,000.
A bikin zagayowar ranar cutar ta shekarar data gabata kungiyar kwarrun Likitocin Kiwon Lafiya ta kasa NMA, ta nuna damuwarta kan ci gaba da yaduwar cuatar, duk da kokarin da aka yi, na yakarata baki daya a kasar.
Har yanzu a kasar nana, ana ci gaba da samun rahoton masu fama da cutar, a wasu jihohin kasar, inda kuma a wasu kasashe 17, aka samu rahoton ana samun cutar a duk shekara, da ta kai 1,000.
Wasu alkaluma sun nuna cewa, daga 2011 zuwa 2021 a duk shekara ana samu sabbin kwayoyin cutar da suka kai guda 2,754, wanda suka kai kashi 93.
A cewar kungiyar, kashi 8.3 na sabbin kwayoyin cutar, ana samun su ne, a jikin yara ‘yan kasa da shekaru 15, wanda kuma sabbin kwayoyin cutar ke nuna cewa kashi 14.3 ke yanyo nakasa, wanda hakan ya nuna cewa, hakan ya faru ne, saboda jinkirin daukar matakan duba lafiyar wadanda suka kamu da kwayar cutar.
Bisa wasu alkamuna da Shirin Dakile Yaduwar Cutar Fuka da Kuturta ta kasa NTBLCP da kuma Shirin Buruli da ke Dakile Ciwon Ulcer ya fitar a 2022, sun nuna cewa, an samu sabbin kwayoyin cutar da suka kai 2393, a shekarar 2022, inda aka samu mata kashi 37, na dauke da kwayoyin cutar yara kuma kasa da goma na dauke da kwayoyin cutar.
Hukumar WHO ta bayyana cewa, akasari cutar ta fi shafar Ftar jikin bil Adma ne wacce kuma take janyowa wanda ya kamu da ita, nakasa, idan har ba a yi masa magani ba.
A cewar WHO, ana kamuwa da cutar na yazuwa ne daga Hanci da Bakin wanda ya kamu da ita.
Ana warke wa daga cutar, ta hanyar yin amfani da magungunan da ake yakarta da kuma yin gwaje-gwaje.
Sai dai, wadanda suka kamu da cutar, suna yin jinkirin zuwa a yi masu gwajinta, musamman domin kar a rinka nuna masu kyama.
Bikin ranar ya yi daidai da manufar cimma burin karnin rayuwa wato (SDGs).
Ranar ta kasance mai matukar mahimmanci wanda taron ke hado kan kwararu a fanin kiwon lafiya domin tattaunawa kan cutar.