Gabanin ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba da za a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya na shekarar 2022 a kasar Qatar, an bukaci magoya bayan Nijeriya da za su je kasar domin kallon wasan kwallon kafa da su mutunta ka’idoji da dokokin kasar.
Ofishin Jakadancin Nijeriya a Doha ya ba da wannan shawarar a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce ya kamata magoya bayan Nijeriya su yi kokarin yin biyayya da kuma mutunta dokokin kasar da ke karbar bakuncin tawagar kwallon kafa ta duniya.
Har ila yau, ya gargadi magoya bayan Nijeriya da cewa, Visa din da aka basu mai suna Hayya card, anyi ta ne don zuwa kallon wasannin kawai ba don zama ko aiki a kasar ta Qatar ba.
Sanarwar da mai magana da yawun ofishin Mista Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu ta ce: “Ofishin jakadancin Nijeriya a Doha na kasar Qatar yana maraba da magoya bayan Nijeriya da za su je gasar.
“Ofishin Jakadancin yana so ya ba da shawara mai karfi cewa magoya bayan Nijeriya masu tafiya don wasan kwallon kafa ya kamata su yi kokari su mutunta dokokin kasar Qatar mai masaukin baki.”