ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gasar NPFL: Kano Pillars Da Enyimba Sun Raba Maki

by Rabilu Sanusi Bena
4 weeks ago

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da takwararta ta Enyimba International sun tashi canjaras 0-0 ba tare da an jefa ƙwallo a raga ba, a wasan mako na shida na gasar Firimiyar Nijeriya (NPFL) da aka fafata a Filin Wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a Birnin Kano.

Ƙungiyoyin biyu sun shiga fafatawar ne da burin samun nasara mai muhimmanci, inda Enyimba ta ziyarci Kano da fatan samun maki uku domin barin ƙasan teburin gasar, yayin da Pillars kuma ke fatan samun nasara domin haurawa zuwa matsayi na biyu, sai dai dukkaninsu sun gaza cimma wannan buri.

A yayin da ake tsaka da fafatawa a minti na 56 da fara wasan, alƙalin wasa ya dakatar da karawar na ɗan lokaci sakamakon wata iska mai ƙarfi da ta taso, kafin daga bisani aka ci gaba da taka leda bayan kusan mintuna 10 da lafawar iskar.

ADVERTISEMENT

Wannan sakamako ya sa Kano Pillars ta ci gaba da zama a matsayi na shida a kan teburin gasar da maki tara a wasanni biyar da ta buga, yayin da Enyimba ta ci gaba da maƙalewa a matsayi na ƙarshe da maki ɗaya kacal.

A wasanninsu na gaba, Kano Pillars za ta karɓi baƙuncin Sporting Lagos a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, yayin da Enyimba za ta karɓi baƙuncin Shooting Stars ta Ibadan a filin wasa na Enyimba International a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba.

LABARAI MASU NASABA

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Abubuwa 3 Da Za Su Sa Ɗan Wasa Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Bana

MASU ALAKA

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa
Wasanni

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal
Wasanni

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Wasan Bayern Munich Da Arsenal

October 21, 2026
Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona
Wasanni

Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Wasan PSG Da Barcelona

October 20, 2026
Next Post
Atiku Ya Sha Alwashin Ƙarin Albashi A Ranarsa Ta Farko

Atiku Ya Sha Alwashin Ƙarin Albashi A Ranarsa Ta Farko

LABARAI MASU NASABA

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

Babban Jami’in Diflomasiyya Na Kasar Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Jamhuriyyar Congo

October 23, 2026
Gwamnatin Kano Ta Rufe Asibitocin Kuɗi 35

2027: Tinubu Zai Samu Ƙuri’u Masu Yawa A Kano – Gwamna Yusuf

October 23, 2026
Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.