Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata na ƙasa, yana mai bayyana cewa tsadar rayuwa ta lashe darajar albashin N70,000 da ake biya a yanzu.
A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, Atiku ya bayyana cewa a kan farashin mai na N1,400 kowace lita, albashin N70,000 na wata ɗaya litar mai 50 kacal zai iya saya, saɓanin tsohon albashin N30,000 da ke sayen lita 118 a shekarar 2023.
Gwamnatin Tarayya dai ta amince da ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa N70,000 ne a watan Yulin 2024 bayan doguwar tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago, tare da alƙawarin sake duba shi bayan shekaru uku. Sai dai Atiku ya jaddada cewa halin ƙuncin da ma’aikata ke ciki sakamakon tashin farashin abinci, gidajen haya, wutar lantarki da sufuri ya nuna cewa wannan ƙarin bai samar da sauƙin da ake buƙata ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙalubalanci Tinubu da ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan sake ƙara albashi maimakon ɓata lokacin ƙungiyar ƙwadago ta NLC da sauran shugabannin ma’aikata da tarurrukan da ba su da tabbas. Ya kuma nuna cewa ƙarancin albashin Nijeriya bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta shi da na sauran ƙasashen Afirka masu arziƙin man fetur kamar su Aljeriya da Gabon.
A ƙarshe, Atiku ya yi alƙawarin cewa idan har aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027, gwamnatinsa za ta fara aikin ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata tun daga ranarsa ta farko a ofis, tare da samar da tsarin tallafi na musamman ga man fetur ɗin da ake tacewa a cikin gida domin rage wa al’umma raɗaɗin tsadar rayuwa.














