Ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya karya tarihin Kylian Mbappe na zama matashin dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Zakarun Turai kafin ya kai shekaru 20.
Yamal mai shekaru 19 ya cimma wannan nasara ne bayan zura kwallo a ragar Aston Villa a wasan da Barcelona ta ci 3-0 a ranar Talata, inda ya kai kwallaye 14 a gasar.
Kafin wannan lokaci, Mbappe ne ke rike da tarihin da kwallaye 13 kafin ya cika shekaru 20. Duk da cewa dan wasan na Real Madrid ya ci kwallaye 72 a gasar baki daya, Yamal ya zarce shi a wannan fanni.
Yamal ya kafa sabon tarihin ne a wasanni 37 da ya buga a gasar Zakarun Turai. Haka kuma, shi ne matashin dan wasan da ya fara taka leda a gasar.













