Al’ummar Awka tashi cikin rudani a garin Amansea da ke Karamar Hukumar Awka ta Arewa a Jihar Anambra kan bacewar gawar wani dattijo a cikin al’ummar, mai suna Pa Micheal Nwanwuba Onyekwelu, daga dakin ajiyar gawa.
Marigayi Pa Onyekwelu mai shekaru 115, wanda shi ne mutum mafi girma a garin Amansea ya rasu kuma an ajiye gawarsa a wani asibitin Regina da ke garin domin shirin gudanar da jana’izarsa a gidan dangin marigayin da ke unguwar Orebe a karamar hukumar.
- Shugabancin Majalisa Ta 10: Ko ‘Yan Mowar APC Za Su Kai Bantensu?
- Manyan Jami’an Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Game Da Alakar Kasashen Biyu
Bugu da kari, an kammala shirye-shiryen bikin jana’izar tare da farkawa da masu tausayawa za su gudanar a ranar Alhamis a gidan iyali yayin da ake gudanar da hidimar coci, da kuma bayar da horo kan hakan, da ya kamata a yi a makon jiya Juma’a.
Duk da haka, mambobin al’umma da masu goyon baya ciki har da gungun limaman coci sun hallara, da al’ummar Cocin Katolika na Saint Anthony.
Amansea, shi ne wurin da za a binne gawar, amma an neme ta an rasa. Bincike ya nuna cewa iyalin wani mamaci ne da ba a bayyana ko su waye ba daga garin Nsuka, Jihar Enugu suka yi kuskuren daukar gawar a madadin gawar mahaifinsu da suke zaton shi ne a wurin.
Sun ajiye gawar mahaifinsu bisa kuskure sun tafi da gawar marigayi Pa. Onyekwelu kuma tun daga lokacin suka binne shi makonni biyu da suka gabata kafin ainihin danginsa su zo daukar gawar a makon jiya Juma’a.
Kokarin samun daya daga cikin ‘ya’yan mutumin da zai yi magana kan lamarin ya ci tura.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa an tono gawar Pa Onyekwelu inda aka dauke shi
domin komawa da shi al’ummarsa ta Orebe domin binne shi a yammacin ranar Asabar da ta gabata.