Wata gidauniyar kasar Qatar mai suna ‘Education Above All Foundation (EAA)’ ta ware Naira Miliyan 332.8 don tallafa wa yara fiye 20,802 da suke gararamba a titi ba tare da zuwa makaranta ba a fadin Jihar Katsina.
Wakiliyar kungiyar majalisar dinkin duniya ta (UNICEF) a Jihar kano, Misis Rahama Rihood, ce ta bayana haka a yayin kaddamar da shirin tallafa wa mutanen karkara da aka yi a karamar hukumar Mani ta Jihar Katsina.
- Hajjin 2022: Matawalle ya bukaci maniyyata su yi wa Najeriya addu’a ta musamman kan matsalar tsaro
- Ya Kamata A Sanya Binciken Kare Hakkin Dan Adam A Amurka Cikin Ajanda
Ta ce, tuni aka kaddamar da tallafin bayar da agajin kudin a jihohin Katsina, Kebbi, Sakkwato da kuma Jihar Zamfara.
Ta kuma kara da cewa, a karkashin shirin an ware Naira miliyan 332,832.000 don taimaka wa yara ‘yan makaranta 20,802 a kananan hukumomi Kafur, Mani da Safana da ke Katsina.
“Za a bayar da kudaden ne ta hannun iyaye mata 10,557 don taimaka wa yaransu komawa makaranta don cigaba da karatu.
Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari, ya yaba wa gidauniyar, inda ya ce shirin tallafin zai matukar taimaka wajen bunkasa harkar ilmi a fadin jihar.
Ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan taimakon da ake bukata don samun nasarar shirin.