A wani bangare na kokarin ba ‘Yan Jarida horo kan dabarun aiki da gogewa a bangaren aikin Jarida, Gidauniyar Daily Trust Foundation masu tashar Trust TV da wallafa Jaridar Daily Trust da Aminiya tare da tallafin Gidauniyar MacArthur sun horar da ‘Yan jarida a Kano.
Horon na kwanaki uku, wanda aka zabo ‘yan jarida kusan 30 daga gidajen jaridu da gidajen rediyo da talabijin daga yankin Arewa maso Yamma, ya ta’allaka ne kan bin diddigin kasafin kudi da kuma binciken yadda ake kashe kudaden al’uma a gwamnatance.
- Adamu Ya Kori ‘Yan Jarida Daga Ofishin APC Bayan Tutsun Da ‘Yan Jam’iyyar Suka Tayar
- ‘Yan Sanda A Jihar Osun Sun Bindige ‘Yan Jarida 2 A Lokacin Zanga-zanga
Da yake gabatar da jawabin bude taron, shugaban gidauniyar Daily Trust, Malam Bilya Bala, ya ce horon wani bangare ne na manufofin gidauniyar na kara kwazo ga ‘yan jarida a fadin Nijeriya.
“Abin takaici a cikin ‘yan shekarun nan, mun ci karo da wasu ‘yan jarida da suka bayyana cewa tun bayan kammala karatunsu ba su taba halartar wani horo ba sama da shekaru goma bayan kammala karatun jami’a. Abin ban mamaki ne wannan,”
“Gidauniyar mu a shirye take ta sauya wannan dabi’a, kuma shi ya sa muka tsakulo ‘Yan Jarida daga kafafen yada labarai daban-daban, ba wai Daily Trust kadai ba, domin ku ci gajiyar wannan bita,”
“Muna sha’awar horar da ‘yan jarida daga tushe domin aikin jarida a yanzu ya fi na baya fiye da kowane lokaci, a wannan zamani na kafofin watsa labarai na zamani,”
“Binciken kasafin kudi yana da matukar muhimmanci a yunkurinmu na yi wa gwamnati hisabi ga jama’a da kuma mai da hankali kan gaskiya a harkokin mulki a Nijeriya,”
“Ana fitar da kudade mai yawa daga Abuja zuwa jihohi da kananan hukumomi; mataki na biyu da na uku na gwamnati na karbar haraji da kudaden shiga daban-daban, wanda ba kasafai suke kashe wa jama’a ba.”
A nasa bangaren, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba, wanda Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Inuwa Yakasai ya wakilta, ya gode wa wadanda suka shirya wannan taro da ya bayyana a matsayin taron ga jama’a masu kishin kasa wadanda a kodayaushe suke tabbatar da cewa an samu nagartaccen aiki.
Ya ba da tabbacin gwamnatin jihar Kano a shirye ta ke ta ci gaba da bayar da hadin kai da bayar da kwarin guiwa a wannan fanni.
Wadanda suka jagoranci horon sun hada da tsohon kwamishinan kudi na jihar Kano, Farfesa Kabir Isah Dandago da Daraktan Gidauniyar Daily Trust, Theophilus Abbah da kuma Caheles Mba daga kamfanin Dataphyte da Atiku Samuel da dai sauransu.