Gidauniyar Aliko Dangote da hadin guiwar Gwamnatin jihar Kano, asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da kuma gidauniyar Bill and Melinda Gates sun rabba hannun yarjejeniyar fahimtar juna domin yin aiki tare wajen yaki da cutar Tamowa da yara ke fama da shi sakamakon karancin samun abinci mai gina jiki a jihar Kano.
Baya ga bangaren kula da cutar Tamowar, bangarorin za kuma su taimaka wajen inganta kiwon lafiya a jihar tare da kula da yin rigakafi a kai a kai domin kyautata kiwon lafiya musamman na yara da mata.
Jimkadan bayan rabbata hannun a ranar Laraba da ya gudana a fadar Gwamnatin jihar Kano, babban darakta mai cikakken iko na gidauniyar Dangote, Zouera Yousefou, ta taya Gwamnatin jihar Kano murnar kawowa wannan matakin da kuma irin nasarorin da aka samu tun lokacin da suka fara sanya hannun yarjejeniya na farko a 2013 da na biyu a 2017 har zuwa yanzu da suka sake sanya hannu a mataki na uku.
Misis Yousefou ta kuma jinjina wa Gwamnatin Kano din bisa ririta kudaden da aka ware na rigakafi kan hakan ya ce jihar ta samu karin kaso domin kara mata azama kan wannan fannin.
MD/CEO ta kuma kara da cewa bangarorin abokan jeren sun samu nasarori sosai wajen rage kaifin mace-macen mata masu juna biyu da yara a jihar.
Ta ce jami’ansu na sanya ido domin ganin ana tafiyar da lamura yadda suka kamata. Ta nemi sarakunan gargajiya da su kara himma wajen fadakar da al’ummar su muhimmancin kiwon lafiya da amsar rigakafi, abinci mai gina jiki, kula da mata masu juna biyu da sauran bangarorin lafiya.
Ta bada tabbacin gidauniyar nasu na cigaba da taimakawa a fannin kiwon lafiya musamman na yara da mata.
A nashi jawabin, gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jihar ta samu nasarori masu tarin yawa a bangaren kula da lafiyar al’umma.
A cewarsa, gwamnatinsa ba ta wasa sako-sako da harkar kiwon lafiya a kowani lokaci ta hanyar inganta kanana da manyan asibitin kula da lafiya tare da samar da wadatatun ma’aikatan da za su kula da su.
Ganduje ya ce hatta sanya hannun yarjejeniyar na nuni da himmatuwar Gwamnatin ne a bangaren kiwon lafiya.
Ya tabbatar da cewa jihar da ta kula da tallafin da ta samu daga abokan jere domin cimma manufofin da aka sanya a gaba. Sai ya gode musu bisa hakan tare da basu tabbacin kokarin gwamanti a kan hakan.
Tun da farko daraktan gidauniyar Bill and Melinda Gates a Nijeriya, Jeremie Zoungrana, ya nuna farin cikinsa bisa shaida sanya hannun da suka yi