Khalid Idris Doya" />

Gidauniyar Yaki Da Talauci Ta Kasar Sin Ta Taimaka Wa Mutum Miliyan 30

Gidauniyar yaki da talauci ta kasar Sin CFPA, ta taimakawa mutane sama da miliyan 30 tun bayan kafuwarta shekaru 30 da suka gabata.
Majiyoyi daga gidauniyar na cewa, ya zuwa karshen 2018, gidauniyar ta samar da tallafin da darajarsa ta kai sama da yuan miliyan 5.85 kwatankwacin dala miliyan 871, ciki har da tsabar kudi.
Gidauniyar ta kuma taimaka wajen raya sana’o’i a yankuna domin karawa mutane kudin shiga.
Bugu da kari, tun daga shekarar 2015 zuwa yanzu, ta kashe yuan miliyan 11.67 a fannin cinikayya ta intanet, domin taimakawa manoma 16,000 sayar da amfanin gonarsu. Kimanin mutane 59,000 ne suka amfana daga ayyukan gidauniyar na raya harkokin bude ido, yayin da ta bada rancen sama da yuan biliyan 40.7 domin bunkasa ayyukan manoma.
Ita kuwa kyautar ‘Lobe Package’ wato ‘kunshin soyayya ko kauna’ da ta fi shahara cikin ayyukan gidauniyar, na ba masu bada tallafi damar aikewa da kyaututtuka domin taimakawa dalibai a yankuna masu fama da talauci. Shirin ya samu kyaututtuka dai-dai har guda miliyan 3.706, kana ya zuwa karshen 2018, kudin da ya samu ya kai yuan miliyan 677.

Exit mobile version