• English
  • Business News
Friday, July 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gimbiya Sirindhorn Ta Thailand:Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Inganta Hadin Gwiwar Al’ummun Kasa Da Kasa

by CGTN Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Gimbiya Sirindhorn Ta Thailand:Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Inganta Hadin Gwiwar Al’ummun Kasa Da Kasa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

A kwanakin baya ne, gimbiya Maha Chakri Sirindhorn ta kasar Thailand, ta yi tsokaci kan muhimmancin shawarar “Ziri daya da Hanya Daya” da kasar Sin ta gabatar, yayin wata hira da wakiliyar gidan telabijin na CGTN a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Ta bayyana cewa, layin jiragen kasa tsakanin kasashen Sin da Laos da Thailand da aka gina karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” yana da muhimmanci matuka, domin gina layin dogon zai inganta ci gaban tattalin arziki. Ta hanyar hada layin dogon, mu’amalar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Thailand da Sin za ta ci gaba da karuwa, kuma jama’ar Thailand da ta Sin za su iya yin hadin gwiwa wajen zuba jari a wasu ayyuka.

  • San Francisco Sabon Mafarin Hadin Gwiwar Sin Da Amurka Ne
  • Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi Yayin Kwarya-kwaryar Taron Shugabannin APEC

Ta kara da cewa, a halin yazu, layin jiragen kasa tsakanin Sin da Laos ya hada wurare daban daban na kasashen 2, kuma ya hada Turai dake yammacin duniya. Kana a nan gaba, za a hada layin jiragen kasa na Sin da Thailand da layukan dogo da aka gina a baya.

Gimbiya Sirindhorn ta yi imani cewa, ba ma kawai layin jiragen kasa na Sin-Laos-Thailand zai inganta ci gaban tattalin arzikin kasashen ba, har ma zai taimakawa raya tattalin arzikin sauran kasashe. Shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta ba al’ummun Thailand da Sin da na kasashe daban daban damar yin hadin gwiwa tare. Ta wannan shawara, Sinawa da dama sun zo Thailand don zuba jari, a sa’i daya kuma mutanen Thailand masu yawa sun je Sin don zuba jari. Ban da zuba jari a fannin cinikayya, shawarar ta taimaki jama’a wajen samun saukin tafiye-tafiye da yawon shakatawa. Saboda haka wannan shawara ce mai kyau, wadda ke da ma’ana sosai.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: San FranciscoShawarar ziri dayaThailand
ShareTweetSendShare
Previous Post

Duniya Na Fatan A Tabbatar Da Daidaiton Da Aka Cimma A San Francisco

Next Post

Mu Kula Da Rayuwar ‘Ya’ya Mata Masu Shaye-Shaye (II)

Related

Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita
Daga Birnin Sin

Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

11 hours ago
Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL
Daga Birnin Sin

Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

12 hours ago
Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori
Daga Birnin Sin

Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

13 hours ago
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

15 hours ago
An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing

16 hours ago
UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba
Daga Birnin Sin

UNHRC Ta Zartas Da Kudurin Sin Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam Ta Hanyar Samun Ci Gaba

1 day ago
Next Post
Mu Kula Da Rayuwar ‘Ya’ya Mata Masu Shaye-Shaye (II)

Mu Kula Da Rayuwar 'Ya'ya Mata Masu Shaye-Shaye (II)

LABARAI MASU NASABA

NPA Ta Tarbi Babban Jirgin ‘Ruwa MB Ocean Dragon’ Don Bunkasa Ayyukanta

NPA Ta Tarbi Babban Jirgin ‘Ruwa MB Ocean Dragon’ Don Bunkasa Ayyukanta

July 11, 2025
Rikicin Masarautar Kano Ya Kara Zafafa

Rikicin Masarautar Kano Ya Kara Zafafa

July 11, 2025
Yunkurin Magance Matsalar Tsaro Da Rigingimu A Arewa…

Akwai Bukatar Hada Kai Da Aiki Tare Tsakanin Hukumomin Tsaro

July 11, 2025
Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Matakin Kwata Fainal Bayan Doke Botswana

Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Kai Matakin Kwata Fainal Bayan Doke Botswana

July 10, 2025
Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

Mataimakin Babban Magatakardan MDD: Sin Aminiya Ce Da Afirka Za Ta Iya Dogaro Da Ita

July 10, 2025
Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

Li Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da ALLi Qiang Ya Gana Da Manyan Jami’an Masar Da AL

July 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe

July 10, 2025
Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

Yadda JKS Ta Jure Tsawon Tarihin Gwagwarmaya Da Cimma Nasarori

July 10, 2025
An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

An Kama Magungunan Jabu Na Fiye Da Naira Biliyan Ɗaya A Kano

July 10, 2025
Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam

July 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.