Wata gobara da ta tashi ranar Asabar a wani shagon fenti da ke Ilorin ta kone wasu gidaje guda biyu da ke makwabtaka da su tare da lalata kadararar da aka kiyasta kudinta ya kimanin Naira miliyan 39.
Gobarar ta lalata wasu shaguna biyar da ke gefen shagon fenti.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Kwara, Mista Hassan Adekunle, ya bayyana cewa, “kwatsam wani shagon fenti ya kama wuta tare da lalata wasu gidaje guda biyu da aka gina a gefensa.
“Baya ga gine-gine biyu da gobarar ta lalata, wasu shaguna biyar da ke kusa da wurin kuma abin ya shafa.
“Masu kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu gine-gine.
Adekunle ya kara da cewa: “Saboda yanayin fentin wutar ta kara ta’azzara kuma tun farko mutane suka sanar da Hukumar kashe gobara da wuri,” in ji Adekunle.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Kwara, Mista Falade Olumuyiwa, ya kuma bukaci mazauna yankin da su rika kashe na’urorin wutar lantarki a ko da yaushe musamman yayin barin gidajensu da kuma lokacin kwanciya barci domin dakile haduran gobara.