Gobara Ta Kone Shaguna 70 A Kasuwar ‘Yan Katako Ta Kano

Hukumar ‘yan kwana-kwana ta jihar Kano ta bayyana cewa gobara ta kone shaguna 70, a wani waje na wacin gadi da ke kasuwar ‘Yan Katako cikin yankin Rijiyar Lemo ta jihar Kano.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta ‘yan kwana-kwanan Saidu Mohammed ya tabbatar da afkuwar wannan gobara ranar Alhamis din da ta gabata.
Ya ce, shaguna guda 30 sun kone kurmus, yayin kuma guda 40 rabinsu ya cinye, inda jimilla aka samu guda 70 kenan. “Mun samu labarin aukuwar lamarin ne ta waya a ranar Alhamis da misalin karfe 3.45 na dare, ta hannun Bashir Suleiman cewa, wuta ta tashi a cikin kasuwa. Samun wannan labara ke da wuya, nan take muka tura jami’anmu wajen da lamarin ya auku da misalin karfe 3.52 na dare, domin su kashe wannan wuta don kar ta shafi sauran shaguna,” in ji shi.
Ya shawarci ‘yan kasuwa da kuma sauran mutane da su yi taka zan-zan wajen yin amfani da kayayyakin wuta domin kaucewa ga fadawa cikin irin wannan lamari. Mista Mohammed ya kuma shawarci mutane a kan su dunga ijiye abun kashe wuta kusa da su, wanda za su iya amfani da shi idan gobara ta tashi kafin su kira jami’an kwana-kwana. Mohammed ya bayyana cewa, su gudanar da binciken musabbabin wannan gobara.

Exit mobile version