Wata gobara da ta tashi a kusa da Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Yola, ta lalata shaguna 10.Â
Wutar ta tashi ne a ranar Asabar, sai dai an ce kone daji ne ya haddasa gobarar.
- Cire Tallafin Mai: Magani Mai Daci Ga Kashi 99 Cikin 100 Na ‘Yan Nijeriya
- Masarautar Adamawa Ta Naɗa Hakimai 3 A Gundumar Ƙaramar Hukumar Hong
Mataimakin Gwamnan jihar, Farfesa Kaletapwa Farauta, a ziyarar da ya kai wajen, ya gargadi mazauna yankin da su gujewa kone daji.
“Wannan lokacin rani ne, kuma iska na da karfi sosai, ya kamata mutane su daina kone daji ba tare da izini ba.”
“Muna kira ga jama’a da su daina kone daji musamman wanda ke kusa da wuraren zama da shaguna.”
Farfesa Farauta ya bada tabbacin gwamnatin jihar za ta tallafa wa wadanda lamarin ya shafa.
Misis Mercy Paul, wacce shagonta ya kone a gobarar, ta ce ta rasa dukkan dukiyarta a gobarar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp