A kalla mutum 34 ne aka bada labarin cewa sun rasa rayukansu yayin da aka samu tashin wutar gobara a wani wajen ma’ajiyar Mai a Jamhuriyyar Benin yayin da wasu mutum 20 kuma suka samu munanan raunuka.
An ce, wutar ta tashi ne a wata haramtacciyar ma’ajiyar mai da ke Semi-Podji – wani garin da ke kan iyaka da Nijeriya.
- Manyan Hafsoshin Sojin Nijeriya Da Suka Fafata Yakin Biyafara
- Matakan Fara Sana’ar Hakar Ma’adanai Bisa Doka A Nijeriya
Ministan kula da harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin, Alassane Seidou, ya shaida wa ‘yan jarida cewa, jarirai biyu na daga cikin wadanda suka mutu.
“Abun bakin ciki mutum 34 ciki har da jarirai biyu sun mutu. Gangar jikinsu ya kone sakamakon tashin wutar gobarar mai,” Seidou ya shaida.
Ya kara da cewa, a halin da ake ciki wadanda suka jikkata kuma suna kan amsar kulawar likitoci a asibiti.
Duk da cewar ministan bai bada wani karin haske kan masu safaran mai din ba, ana dai yawan samun safaran mai daga Nijeriya zuwa jamhuriyyar Benin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp