Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nuna matuka farin cikinsa bisa yadda ya ce ya gano Jihar Gombe tana kan turbar kawo sauyi a harkar kasuwanci wanda hakan ya kai ga kasancewar ta a matsayin wacce ta yi fintinkau kan sauran jihohi a bangaren saukaka harkokin gudanar da kasuwanci.
Mataimain shugaban kasan wanda ke wannan jawabin a wajen bikin rufe taron zuba jari na Jihar Gombe da ya gudana a makon jiya, ya ce kamar yadda rahoton kwamitin fadar shugaban kasa kan harkokin kasuwanci ya bayyana cewa jihar ita ce jagaba a fannin tsari da kuma saukaka sana’o’i da harkokin kwadago.
Ya ce taron zuba jari irin sa na farko ya dace da kudurin Jihar Gombe na samar da kyakkywan yanayin kai wa ga ci gaba mai dorewa, karuwar arziki, zaman lafiya, hadin kai da ci gaba ga al’ummar jihar, kamar yadda yake kunshe a cikin kundin ci gaba na Jihar Gombe na shekaru goma daga 2021 zuwa 2030.
“Wannan kundin ci gaba, yana daya daga cikin na gaba-gaba da wata jiha ta samar, wadda ya yi cikakken bayani kan kudurori da tsare-tsaren jihar na dogon zango don nausa ta gaba. Baya ga wannan, Gombe ta samar da cikakken tsarin kashe kudade na matsakaicin zango daga 2020 zuwa 2022.”
Yemi Osinbajo ya kara da cewa, “Idan za ku iya tunawa, watanni 18 da suka gabata, na zo nan Gombe don bikin baje kolin kayayyakin da masana’antu karo na 27, inda na ziyarci cibiyoyin matsar mai da sarrafa shinkafa, kuma na ga daruruwan buhunan shinkafa da ake sarrafawa a duk rana.
“To yanzu dai za mu iya bugun kirjin cewa Gombe ta dauki aniyar nausa burin ta na zuba jari zuwa mataki na gaba ta hanyar shirya wannan muhimmin taro. Harkokin kasuwanci na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasarmu.
Wannan ya kara zama abu mai muhimmanci ganin yadda muke da dimbin damammaki musamman ganin yadda aka sanya hannu kan yarjejeniyar harkokin kasuwanci maras ka’idi ta Afirka (AfCFTA).
Mataimakin shugaban kasan ya yi kira ga sauran jihohi da su yi koyi da Jihar Gombe, domin tattalin arzikin kasar nan ya samu hababa, kana ya bayyana godiyarsa ga kamfanonin da suke zuba jari na ciki da waje tare da kiransu da su kara hakan domin ci gaban Nijeriya.