Jama’a barkanmu da Juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a.
Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaiahe-gashensu zuwa ‘yan uwa da abokan arziki na kusa da na nesa. A yau ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gaishen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliya Juma’a tare da kai ziyara lafiya.
Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka.
Sako daga Yusuf Murtala yusuf
Assalamu alaikum! Barkan mu da Juma’a al’ummar Musulmi baki daya da ma’akatan gidan wannan jarida mai albarka. Ina gaida iyayena da ‘yan uwana maza da mata, ina yi musu barka da Juma’a tare da fatan alkhairi Allah ya maimaita mana amin.
Sako daga Muhammad Sani
Assalaikum alaikum al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi, tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya. Ina gaida yayye iyaye da kannensu tare da yi musu fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya Allah ya sa haka amin barka da Juma’a.
Sako daga Aisha Abba muhammad
Ina mika sakon gaisuwata zuwa ga mijina, ina mika sakon gaisuwa ta zuwa ga iyayena da fatan alkhairi tare da fatan suna cikin koshin lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga ‘ya’yana da ‘yan uwa da abokan arziki na gida da na waje da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa zuwa ga daukacin Musulmi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana amin ya Allah.
Sako daga Sunusi Garba
Assalamu alaikum! Ina mika sakon gaisuwa ga ma’aikatan wannan gidan jarida na LEADERSHIP Hausa tare da mika godiya ta da suka bani dama na mika sakon gasuwa na gode.
Ina mika sakon gaisuwa ga iyaye na ina fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan ‘uwana ‘ya’yana da kannena da fatan suna cikin koshin lafiya sun yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga Rabi’atu Abubakar
Assalamu alaikum, ina mika sakon gaisuwata ga mijina ina yi mishi fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da ‘yan uwana da abokan arziki da al’ummar Musulmi baki daya tare da fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana Allah ya kawo mana sauki a rayuwarmu amin.
Sako daga Aisha Ummar
Barkammu da warhaka barkammu da wannan lokaci ina mika sakon gaisuwa ta ga mijina ko na ce wanda zan aura da fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Ina mika sakon gaisuwata ga iyaye da yayye da kannena ‘yan uwa da abokan arziki tare da fata alkhairi Allah ya maimaita mana.
Sako daga Rahma Babangida
Assalamu alaikum!
Ina mika sakon gaisuwa ga mutanan wannan gidan jarida mai albarka ina musu barka da Juma’a, ina gaida iyaye na gida da na waje yayye da kannena ‘yan uwa da abokan arziki duka ina muku fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.