Jama’a barkammu da juma’a, barkanku da kasancewa tare da wannan shafi na Goron Juma’a. Shafin da ke ba wa kowa damar mika sakon gaishe-gashensa zuwa ga ‘yan uwa da abokan arziki na kusa, da na nesa. A you ma ina dauke da wasu sakonnin gashe-gashen, sai dai kuma kafin na je ga sakonnin masu karatu da suka aiko, sai na fara da mika tawa gaisuwar zuwa ga dukkannin ma’aikatan wannan gidan jarida mai albarka ta LEADERSHIP HAUSA, musamman ma Editana Abdulrazak Yahuza Jere, da fatan an yi sallar juma’a lafiya, kuma da fatan an yi kwalliyar juma’a ana kuma kai ziyara lafiya. Sai sakonnin da kuka aiko kamar haka:
Sako daga Asma’u Usman:
Assalaikum alaikum!
Al’umar musulmi, ina yiwa kowa fatan alkhairi tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyaye na mama da babana ina musu fatan alkhairi da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Sannan ina gaida ‘yan uwana yayuna da kanne na da fatan sunyi sallar juma’a lafiya. Ina gaida kannan mamana da kannan babana tare da yi musu fatan anyi sallar juma’a lafiya. Sannan ina gaida ‘yan uwa da abokan arziki da fatan kowa yana cikin koshin lafiya tare da barka da juma’a.
Sako daga Amina Isiyaku
Assalamu alaikum! Ina yiwa ma’aikatan Leadership Hausa barka da juma’a tare da fatan sunyi sallar juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga daukakin musulme baki daya tare da fatan anyi sallar juma’a lafiya. Ina mika dakon gaisuwa ta ga iyaye na da ‘yan uwana da abokan arziki tare da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.
Sako daga khadija Lawan Sambo
Ina mika sakon gaisuwa gaisuwa ta ga iyaye na ina yimusu fatan alkhairi tare da fatan sunyi sallar juma’a lafiya, ina mika sakon gaisuwa ta ga ‘yan uwana yayuna maza da mata kannena maza da mata tare da fatan sunyi sallar juma’a lafiya Allah yasa muga ta wani satin amin.
Sako daga Bilkisu Maharazu.
Assalamu alaikum! Ina yiwa iyaye barka da juma’a da yayata da kuma wannena da ‘yan uwa da abokan arziki ‘yan makarantarmu tun daga kan firamare, dakandare, har yunibasiti duka ina mika muka sakon gaisuwa tare da fatan munyi sallar juma’a lafiya Allah ya maimaita mana.