Jama’a barkanmu da juma’a da fatan kowa zai yi juma’a lafiya, Allah ya karbi ibadunmu Amin.
Kamar kowanne mako wannan shafi na mika sakonnin gaishe-gaishenku ga ‘yan’uwa da abokan arziki domin sada zumunci.
Sai dai kuma ba za mu samu damar bude sakonnin gaba daya ba, za mu bude sako daya ne saboda yana yin filin namu a wannan makon yau.Mako mai zuwa za mu kawo sauran cikin yardar Allah. Gasakon kamar haka:
Sako daga Hadi Tsohon Sarki Daura 8164205067:
Assalam, gaisuwar Goron Juma’a ga mai girma tsohon shugaban NUT na Daura Alhaji kuma Hedimastan Pilot Primary School Daura Alh. Sani Mamman da Mal. Sabi’u da Mal. Musa da Mal. Habu Popula da Mal. Mustapha 1 da Mal Mustapha 2 da Mal. Abdullahi da Mal. Sade da Mal. Hamisu da Mal. Abdulhadi 1 da Mal. Abdulhadi 2 da Malama Sa’ade da Malama Hajara da Malama Fatima Bashar da Malama Amina da Uwata Malama Hajiya Zulai da Malama Aisha da Mal. Alh Amadu Sabi’u ina yi masu fatan alkhai.
Haka nan ina gaishe da mai girma tsohon ma’ajin Nut ta Daura Mal. Abdurrahaman da mai girma sabon shugaban NUT na Daura Mal. Lawal Dan Kazaure ina yi masu fatan alkhairi Allah ya sa su yi Juma’a lafiya amin. Gaisuwar goron juma’a ga mai girma shugaban NUT na Jihar Katsina dan kafin Daura da mai girma shugaban hukumar ilimin firamare na karamar hukumar Daura Alh. Nura Lawal da mai girma Alh. Tijjani Sale da mai girma Alh. Nura Salele da mai girma Alh. Najume da mai girma Alh. Ali Namadi da mai girma Uban dawaki.
Gaisuwar goron juma’a ga mai girma dan Madamin Daura hakimin Dumurkol, Hon. Musa Haro da mai girma wazirin dan madamin Daura Alh. Hamisu Haro da maigirma amanar wakilin dan madamin Daura Hon. Alh. Nasiru Kakah da fatan Allah ya kara musu lafiya, Allah ya kare su daga sharrin makiya, Allah yasa su yi juma’a lafiya Amin.
Sai kuma gaisuwar goron juma’a ga mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari damo sarkin hakuri da mai girma Alh. Mamman Daura da mai girma Abdulkarimu Dauda da mai girma Alh. Sabi’u Tunde da mai girma Subeb ciyaman na jahar katsina Alh. Lawal Buhari da fatan Allah ya kara tsaresu daga sharrin abokan halitta mutum ko aljan, da fatan za su yi juma’a lafiya.