Abba Ibrahim Wada" />

Grealish Ya Amince Ya Koma Manchester United

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa, Jack Grealish, ya amince zai koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyar ta dukufa wajen ganin ya saka mata riga.

Dan wasan dan kasar Ingila, mai shekara 24 a duniya ya zura kwallaye tara a raga sannan ya taimaka an zura guda bakwai a wasanni 27 din daya bugawa kungiyar a wannan kakar da ake bugawa ta bana.

Kungiyoyin Barcelona da Real Madrid da kuma Manchester City ne dai suka shiga zawarcin dan wasan wanda kungiyarsa ta Aston Billa karkashin mai koyarwa Dean Smith tayi masa kudi fam miliyan 60.

Sai dai wasu rahotanni sun tabbata da cewar Manchester United itace kungiyar da dan wasan yake fatan bugawa wasa a kakar wasa mai zuwa kuma tuni aka bayyana cewa ya kulla yarjejeniya da kungiyar.

Rahotanni dai sun bayyana cewa har yanzu babu wata tattaunawa da aka fara tsakanin kungiyoyin Aston Billa da Manchester United amma tuni dan wasan ya bayar da damar a fara Magana domin ganin mafarakinsa ya zama gaskiya.

Tuni aka fara rade radin cewa dan wasan ya fara neman hayar gida a birnin na Manchester a shirye shiryensa na komawa United din kuma ana ganin kociyan tawagar Ingila zai iya gayyatar dan wasan zuwa gasar cin kofin nahiyar turai da za’a buga Grealish Ya Amince Ya Koma Manchester United

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa, Jack Grealish, ya amince zai koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a kakar wasa mai zuwa bayan da kungiyar ta dukufa wajen ganin ya saka mata riga.

Dan wasan dan kasar Ingila, mai shekara 24 a duniya ya zura kwallaye tara a raga sannan ya taimaka an zura guda bakwai a wasanni 27 din daya bugawa kungiyar a wannan kakar da ake bugawa ta bana.

Kungiyoyin Barcelona da Real Madrid da kuma Manchester City ne dai suka shiga zawarcin dan wasan wanda kungiyarsa ta Aston Billa karkashin mai koyarwa Dean Smith tayi masa kudi fam miliyan 60.

Sai dai wasu rahotanni sun tabbata da cewar Manchester United itace kungiyar da dan wasan yake fatan bugawa wasa a kakar wasa mai zuwa kuma tuni aka bayyana cewa ya kulla yarjejeniya da kungiyar.

Rahotanni dai sun bayyana cewa har yanzu babu wata tattaunawa da aka fara tsakanin kungiyoyin Aston Billa da Manchester United amma tuni dan wasan ya bayar da damar a fara Magana domin ganin mafarakinsa ya zama gaskiya.

Tuni aka fara rade radin cewa dan wasan ya fara neman hayar gida a birnin na Manchester a shirye shiryensa na komawa United din kuma ana ganin kociyan tawagar Ingila zai iya gayyatar dan wasan zuwa gasar cin kofin nahiyar turai da za’a buga a bana.a bana.

Exit mobile version