Gudanar Da Tsarin Dimukuradiyya Na Cikin Ayyukan Hukumar Mu –Shugaban INEC

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa aikin su ya haɗa da shirya zaɓuɓɓuka da kuma gudanar da shi kan shi tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya.

Haka kuma ya ce yawan masu zaɓe a Nijeriya ya fi na sauran ƙasashe 14 da ke yankin Afrika ta Yamma baki ɗayan su.

A mujallar INEC da hukumar ta raba ran Asabar, an ruwaito cewa Yakubu ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin da Darakta-Janar na Hukumar yi wa Aikin Gwamnati Garambawul (wato ‘Bureau of Public Service Reforms’), Alhaji Dasuki Arabi, ya jagoranci wasu jami’an sa zuwa hedikwatar INEC da ke Abuja inda su ka kai ziyarar musamman.

A cewar shugaban na INEC, aikin hukumar ya wuce na shirya zaɓe kurum.

Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, “Wannan ita kaɗai ce hukuma a Nijeriya wadda aka ɗora wa alhaki bisa tsarin mulki na yin abubuwa da dama dangane da zaɓuɓɓukan mu da dimokiraɗiyyar mu.

“Mu na aikin da ya zarce na gudanar da zaɓe kaɗai; kusan ma mu ne ke gudanar da ɗaukacin tsarin dimokiraɗiyyar mu.

“Wasu daga cikin ayyukan da mu ke aiwatarwa su ne waɗanda wasu hukumomi da dama a wasu ƙasashen ke aiwatarwa. Amma mu a nan mu ne ke yin komai da komai.

“Girman ƙasar nan da haɗe-haɗen ta su ne su ka kawo dalilan abin da mu ke yi. Yawan masu zaɓe da su ka yi rajista a sauran ƙasashe goma sha huɗu da ke yankin nahiyar Afrika ta Yamma idan an haɗe su a waje ɗaya zai gaza da mutum miliyan 11 na masu zaɓe da su ka yi rajista a Nijeriya.

“Saboda haka, a duk lokacin da mu ka gudanar da zaɓuɓɓuka, kamar a ce an gudanar da zaɓuɓɓukan ne a dukkan faɗin Afrika ta Yamma.”

Exit mobile version