Gurfanar Da Mahadi Shehu Gaban Kotu Ya Fara Warware Zare Da Abawa..!

Yanzu fa muna iya cewa kallon ya koma sama, wai tunda shawo ya dauki giwa, batun takadamar da ke tsakanin gwamnatin jihar Katsina da Mahadi Shehu ya dauki sabon salon fayyace gaskiya.

Mutane da yawa sun nuna rashin hakuri game da abinda suka kira cin kashi da Mahadi Shehu ke yi wa gwamnatin jihar Katsina wanda ya nunata  a matsayin marar gaskiya kuma wai gwamnatin awan igiya ce.

To amma da yake ance rana dubu ta barawo daya kuma ta mai kaya, yanzu labarin ya canza, domin kuwa an zo wajan da halin kuwa zai bayyana, kuma alamu na nuni da cewa wasa zai yi kasa.

Na’am, ba wai za a yanke hukunci bane game da abinda ke faruwa, amma ya zuwa yanzu, jikin magoya bayan Mahadi ya yi sanyi kuma sun fadi ba nauyi game da abinda suka yi zato amma sai gashi gwanin na su ya ba su kafa, ita kuwa gwamnati ta yi shiru ba magana.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ta dade tana nazari da tunanin hanya mafi dacewa da zata bulluwa wannan al’amari domin kuwa tasan abinda ya faru da kuma inda aka nufa.

Saboda haka dole ne gwamnati ta yi taka tsantsan wajan samar da hujjuji da zata kare kanta, da wannan mummunan zargi da neman hasala jama’a  su yi mata tawaye.

Mahadi mutun ne wanda ake zargi ya ci mutunci gwamnati, ya keta alfarmarta ya muzanta ta, ya kawo mata nakasu wajan tafiyar da harkokin ta.

Bisa haka ne take neman kuliya ta bi mata kadin abinda take zargin Mahadi ya yi mata wanda ba dai dai ba, saboda haka yanzu duk wani batun yana hannu kuto da kuma jami’an tsaro, su ke da wuka da nama wajan tafiyar da wannan al’amari.

Sannan yanayin da ake ganin Mahadi yana bayyana a gaban kutuna daban-daban ba za a dora alhakin hakan akan kowa ba sai dai shi kan, domin har yanzu bai bayyana cewa ga abinda wani jami’ain tsaro suka  yi masa.

Masana shari’a sun bayyana cewa yanzu shi Mahaid kamar kwai yake, ana lallaba shi ne ya kai gaban shari’a, saboda hala ita ce ke da ikon yin duk abinda ya da ce wanda bai zabawa dokar Najeriya ba.

Sannan sun yi zargin cewa yanzu fa Mahadi yana neman tausayin al’umma ne, saboda haka dole ya zo da wani salo na dauka hankali, misalin irin abubuwan da ake gani a lokacin bayyanarsa a gaban kotuna.

Ga alamu wasu jama’ar na zargin cewa kila ko an sanya jami’an tsaro sun cutar da shi, mutumin da ake neman bayanai na kare kan daga wajan sa, wannan ba zai taba yi wuwa ba, indai gaskiya ake neman ta bayyana a wannan  al’amari.

Sannan ya kamata jama’a su san wani abu, duk wannan abin da ake sau daya kawai aka gabatar da wasu tuhume-tuhume akan Mahadi  gaban babbar kuton tarayya da ke Kano akwai saura da yawa na can suna jiransa.

Shi kuma Mahadi ya kware wajan bayyana cewa shi ne ke tare da gaskiya, saboda haka baya kwansa  sai da zakara, kuma ya sha fada cewa ya shirya tsaf domin fuskantar duk wata tuhuma a gaban kuliya zai kare kansa.

Sannan a lokuta daban-daban ya sha fadin cewa abubuwan da yake fada duk wanda ya jin abin  bai  yi masa dadi ba, kuma yana jin cewa an yi masa ba daidai ba, ya ce don girman Allah a kai shi kotu domin a can ne gaskiya ke jiran mai ita.

Haka kuma shirun da aka ji gwamnati ta yi yasa wancan magana ta Mahadi ta zama tamkar makami na yakin gwamnatin jihar Katsina tunda ya yi ikirari kuma an dauki lokaci babu wanda ya ce uffan balanta  ass.

To sai dai fa, masu iya magana na cewa akwai ranar da Ya zata gidan kanwa, gashi kuwa an zo wajan, kuto dai an fara ba a san ranar gamawa ba, sannan Mahadi ya fara shige da fice ba a san abubuwan da zai sake dawowa da su ba.

Wannan yasa jama’a da dama suka zuba idonu domin ganin yadda wannan al’amari zai kaya, saboda fada tsakanin gaskiya da karya ba zai taba yin nasara ba, dole gaskiya ta yi nasara akan karya.

Gabatar da Mahadi shehu da aka yi a gaban kutona daban-daban sun bar baya da kura, sun nuna gazawa da rashin tsayuwa akan abu musamman ikirarin da Malam Mahadi yake na cewa ya shirya tsaf.

Anya! Mutumin da yake da hujjoji fiye da dubu ashirin zai bayyana a gaban kuto yana wasa kwaikwaiyo irin na su Dino Maleye, lallai abin ya zo da makuwa, saboda al’amari ya canza salo so sai.

Wannan tasa, yanzu da aka ganshi yana bayyana a wani yanayi na ‘yan wasa kwaikwayo, yana raki da kuka yana neman taimako inda har ta kai yana  kiran sunayen wasu mutane domin neman agajin su.

Babu shakka wannan batun ba tsaya nan ba, zai cigaba da wanzuwa a gaban jama’ar jihar Katsina domin su rabe aya da takuwa game da abinda yake ikirari, wannan tasa dole sai an yi a hankali wajan raba da da uwarsa.

Kamar yadda na ambata abubuwa da dama jama’a suke fatan gani game da wannan al’mari, daga cikinsu kuwa akwai batun cewa wannan rakin da Malam Mahadi ke yi a gaban kuliya shima ya zama wani abu da za  sake yi masa nazari na musamman domin gane gaskiyarsa.

Haka kuma wasu hotona da faifan bidiyo da suka rika yawo a kafar sadarwa ta zamani a yanzu da aka fara wannan shari’a shi ne,  kama suna nuna Mahadi lafiyarsa lau ko ko dai ya samu wata matsala ne?

Idan amsa ita ce ba wanda yasan abinda ya same shi, to lallai mabiyansa da kuma wadanda suke goyan bayansa suna da baban aikin domin ya ba su kafa ya kuma yi masu nisa.

Ranar da aka ji Malam Mahadi yana kakari tamkar wanda za a kashe bayan gabatar da shi a gaban kuton majistire ta 4 da ke Katsina, yasa mutane da dama cikin shakku game da wannan al’amari, domin dai ba su yi  zaton haka ba.

Wasu ma tuni zaton cewa za su ga Malam Mahadi ya bayyana a gaban kotu, da karfinsa ya jira ya ji tuhumar da ake yi masa sannan ya dauka tarin hujjujinsa ya fara kare kansa ko kuma akasin haka.

Sai dai har gobe masana harkokin sharia na ganin wannan sabon salon da Mahadi ya bullo da shi ba zai kai shi tudun mun tsira ba, saboda dai ita shari’a idanunta a rufe suke, mai gaskiya kaiwa take gani, kuma idan za a cigaba da yin haka zata dora hannunta akan gaskiya daga nan komi ya kare wai bori ya kashe boka.

Wannan duniya tana da abin mamaki daga cikin kuwa harda yadda Malam Mahadi shehu ke gudanar da sabon samfirin bayyana a gaban kuliya manta sabo, yanzu dai kallo ya koma sama wai shawo ya dauki giwa.

Kuma gufarnar da shi da aka yi bisa wasu zarge-zarge na nuni da cewa gwamnatin ta shirya kare kanta daga wancan zargi da Mahadi ya yi a baya, abin jira a gani shi ne, yadda wannan al’amari zai kaya. An ce idan tabi daga daga na kurya kan sha kashi. To, Allah Ya sawake.

Exit mobile version