An Gwabza Tsakanin ’Yan Sanda Da Ɗalibai A Osun

Daga Idris Aliyu Daudawa

’Yan sanda sun harbe biyu daga cikin ɗalibai masu karatu a kwalejin ilmi ta Ila Orangun hakan kuma yasa suka samu raunuka, a Osogbo ranar litinin, lokacin da suka shiga cikin sahu na ‘yanuwansu ɗalibai daga wasu makarantu, mallakar jihar, suna zanga zangar n domin nuna rashin jin daɗisu akan ƙarin kuɗin makaranta, da masu gudanar da mkarantun suka bada sanarwar ƙarin kuɗin makaranta, a dukkan makarantun da suke ƙarƙashin gwamnatin .

Ɗaliban sun yi dandanzo ne a wani mashahurin wuri da aka fi sani wato wata mararabar Olaiya inda daga can ne suka yi jerin gwano, suka wuce ta hanyar Gbogan/Osogbo , suna yin waƙe waƙe, inda suke la’antar gwamnan da jin haushi abinda da yai masu na ƙarin kuɗin makaranta.

Ɗalibai su suka fara tsokanar ‘yan sanda , inda su kuma daga sai kuma mayar da aro, wajen yin amfanin da Barkonon tsohuwa, suka samu damar wata ɗaliban.

Barkonon tsohuwar da aka harba sai cikin tsautsayi sai ya bugi idon wani ɗalibi da ake kira Azeez, wanda yake a shekara ta farko a sashen harsuna yana kuma karanta Turanci ne wato English, sai kumawani ɗalibi da ak kira Femi shi kuma Barkonon tsohuwar ya same shi ne a kan shi, duk shi ma daga kwalejin ilmi ta Ila Orangun ya ke.

Ɗaya daga cikin ɗaliban masu zanga zangar ya bada sanarwa an kai Femi Asibiti, an kuma sallame shi. Shi kuwa Azeez an mai da shi Asibitin koyarwa na Jami’ar Obafemi Awolowo Ile Ife, don a ƙara duba ma lafiyar shi idon.

Wasu daga cikin ɗaliban wanda ya zo ne daga makarantar Fasaha ta jhar Osun, cewar an ƙara kuɗin makaranta, daga naira dubu Talatin da huɗu zuwa naira dubu sittin da biyar .

Gamayyar ɗaliban sun nuna rashin jin daɗinsu, har suna tunanin wai mi ma yasa ita gwamnatin ta ƙara masu kuɗin makaranta, bayan ita kuma gwamnatin tana biyan Iyayensu rabin albashi.

Mataimakin mai kulawa da sashen Kudu maso Yamma na ƙungiyar ɗaliban Nijeriya, Saheed Afolabi ya shaisa ganin ɗaliban biyu, waɗanda ‘yan sanda suka  harbe shi.

Exit mobile version