Gwamna Bagudu Ya Jajanta Wa ‘Yan Kasuwar Kamba A Kan Gobarar Da Aka Yi

Daga Umar Faruk Birnin Kebbi

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya jajanta wa al’ummar garin Kamba a karamar hukumar Dandi bisa gobarar da ta tashi a babbar kasuwar garin Kamba.

Gwamnan ya kuma bayar da umarnin gaggawar sake gina shaguna da rumfunan da gobara ta shafa ba tare da bata lokaci ba.

Bugu da kari, gwamnan ya bayar da umarnin a kai agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Sanata Atiku Bagudu ya bada umarnin ne a lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnati mai karfi zuwa garin na Kamba da ta kai ziyarar jaje.

Gwamna Atiku Bagudu wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamnan Jihar Kebbi, Kanar Sama’ila Yombe Dabai mai ritaya, ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Dandi kan wannan mummunan lamari da ya shafe su.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta kawo dauki cikin gaggawa ga wadanda abin ya shafa domin rage asarar da suka yi don basu damar ci gabada sana’o’insu kamar yadda suka saba.

Mataimakin gwamnan tare da rakiyar manyan jami’an gwamnati sun duba shagunan da rumfunan da suka kone tare da yi wa ‘yan kasuwar jawabi a wurin da gobarar ta tashi.

A nasa jawabin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi Rt. Hon. Muhammadu Lolo, ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya biya su da yawa ya kuma kiyaye faruwar hakan a nan gaba.

Shugaban majalisar ya ce Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya umarce su da su zo Kamba domin nuna juyayi, wadda za ta hada da ziyarar da gwamnan zai kai garin bayan ya dawo daga aiki a Abuja.

Hakazalika, Shugaban Hukumar Kwadago ta Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Bello Dantani, ya yi jawabi ga ‘yan kasuwar, inda ya yi addu’ar Allah ya yaye mana irin wannan bala’i a nan gaba.

Daga bisani tawagar mai girma ta koma fadar Sarkin Shiko Kamba, Alhaji Muhammadu Zarumai, wanda ya zagaya da mataimakin gwamnan da mukarrabansa a kan shagunan da aka lalata a kasuwar.

A fadar Sarkin Shiko, mataimakin gwamnan, ya mika sakon ta’aziyyar gwamnan, inda ya ce, “Gwamnan ya yi bakin ciki da afkuwar gobarar da ta faru, kuma ya ba da umarnin sake gina shagunan da abin ya shafa cikin gaggawa,” in ji shi.

Da yake mayar da martani, Sarkin Shikon Kamba, Alhaji Muhammadu Zarumai, ya gode wa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu bisa yadda yake nuna soyayya da kulawa ga al’ummar Kamba.

Ya kuma bukaci wadanda gobarar ta shafa da su daure su jira matakan agajin gwamnati.

A wata hira da manema labarai a fadar, sakataren gwamnatin jihar, Babale Umar Yauri, ya bayyana cewa ana shirin samar da motocin kashe gobara a garin Kamba.

daya daga cikin masu shagunan da gobarar ta shafa, Alhaji Abubakar Muhammad ya yabawa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da ya mayar da martanin gaggawa.

Mataimakin Gwamnan ya samu rakiyar Shugaban Majalisar, Alhaji Muhammad Lolo, SSG Babale Umar Yauri, PA ga Gwamna Alhaji Farouk Musa Yaro, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar, Abubakar Muhammad Kana, Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar. , Arewa, Alhaji Sahabi Lolo, shugaban kungiyar dattawan APC, Alhaji Sani Hukuma Zauro, da kwamishinonin noma, albarkatun ruwa, kasuwanci, da ayyuka na musamman.

Sauran sun hada da: Alhaji Hussaini Kangiwa, Shugaban Hukumar Nakasassu na kasa, Alhaji Bello Dantani, Shugaban Hukumar Kwadago kai tsaye, Alhaji Abubakar Nayaya, Shugaban Hukumar Ma’aikatan Kananan Hukumomi, Mai Ba da Shawara ta Musamman kan Tsaro, Garba Rabiu Kamba da Alhaji Faruk Kuru.

A jimilce shaguna da rumfuna ashirin da daya ne gobarar ta shafa, amma ba tare da asarar rayuwa ko rauni ba.

Har yanzu ba a kididdige yawan kayayyakin da gobara ta kone.

Exit mobile version