• English
  • Business News
Saturday, August 2, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal Ya Jaddada Ƙudirinsa Na Tsaron Rayukan Al’ummar Zamfara

by yahuzajere
1 year ago
in Labarai
0
Gwamna Dauda Lawal Ya Jaddada Ƙudirinsa Na Tsaron Rayukan Al’ummar Zamfara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A faɗi-tashin da yake yi wajen samar da ingataccen tsaro, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar Jihar Zamfara.

A ranar Talatar nan ne gwamnan ya halarci bikin yaye wasu dakaru na musamman, waɗanda ke ƙarƙarshin Hukumar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ake kira ‘Agro Rangers’ a Jihar Zamfara.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, dakarun na ‘Agro Rangers’, jami’ai ne na musamman a Hukumar ta Sibil Difens, waɗanda suka samu horo mai zurfi.

Ya kuma ƙara da cewa, an horar da jami’an na musamman a shirye-shiryen gudanar da aikin haɗin gwiwa a yaƙi da ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

Tsaro

Labarai Masu Nasaba

Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa

Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

A yayin jawabinsa a wajen bikin, gwamna Lawal ya yaba wa hukumar NSCDC bisa wannan shiri nasu. Ya ce, “Wannan ya zo ne a wani muhimmin lokaci kuma ya yi daidai da ƙudurinmu na ɗaukar ingantattun matakan yaƙi da rashin tsaro.

“Mun ɗauki wannan a matsayin babban mataki na tunkarar ƙalubalen da ya kawo cikas ga al’ummar mu wajen ayyukan noma, sana’o’in dogaro da kai, da sauran hanyoyin samar da abinci a jihar.

“Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana harkokin tsaro da noma a matsayin muhimman abubuwan da suka sa a gaba. Mun ɓullo da matakai daban-daban don magance ƙalubalen tsaro da kuma bunƙasa noma a jihar. Don haka, muna kallon wannan shiri na jami’an Hukumar Sibil Difens a matsayin wani gagarumin mataki na ci gaba da ɗaukar matakan tsaro da muke ɗauka a matsayin gwamnati tare da jami’an tsaro da ke aiki a jihar.

Tsaro

“A matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da bada haɗin kai da cibiyoyi, ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane wajen yaƙi da duk wani nau’in miyagun laifuka. Mun himmatu wajen samar da tallafin da waɗannan cibiyoyi da ɗaiɗaikun mutane ke buƙata don gudanar da ayyukansu. Manufar farko ita ce tabbatar da tsaron al’ummominmu da kuma sanya su cikin aminci don ayyukan zamantakewa da tattalin arziki wanda zai sauƙaƙe ci gaban jihar da jama’a.

“Ina matuƙar fatan shirin hukumar NSCDC na samar da wani dakarun na musamman, wanda hakan zai samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, musamman waɗanda suka shafi harkar noma.

“Ina da alfahari da ƙaddamar da wannan dakaru. Ina yi muku fatan alheri bisa sauke nauyin da aka ɗora muku. Ina roƙon Allah Ya tsare ku, sannan Ya yi muku jagoranci.”

Tun da farko, Kwamandan Rundunar Sibil Difens a Jihar Zamfara, Kwamanda Sani Mustapha, ya gode wa Gwamna Lawal da gwamnatin Jihar bisa tallafin da suka ba shirin horarwa da dakarun Agro Rangers.

Tsaro

“Yallabai, ɗimbin goyon bayan da ka ke baiwa rundunar ta sa muka kai ga haka. Muna godiya ƙwarai da gaske,” inji shi.

Kwamandan ya ƙara da cewa, Hukumar ta NSCDC ta himmatu wajen samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice a yankunan da ake fama da rikici.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Dauda LawalJami'an TsaroTsaroZamfara
ShareTweetSendShare
Previous Post

Hadin Gwiwa Da Sin Ya Ba Matasan Kasashen Afirka Karin Damammakin Raya Kai

Next Post

Hajj 2024: Jihar Kaduna Ta Kammala Jigilar Maniyyata Fiye Da 4,000 Zuwa Saudiyya 

Related

Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa
Labarai

Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa

26 minutes ago
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
Labarai

Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

11 hours ago
Tinubu Ya Sauke Gawuna A Matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwar BUK, Ya Maye Gurbinsa Da Kaita 
Manyan Labarai

Tinubu Ya Sauke Gawuna A Matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwar BUK, Ya Maye Gurbinsa Da Kaita 

12 hours ago
Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Barazanar ɗorewar Wutar Lantarki A Nijeriya – Minista
Labarai

Bashin Naira Tiriliyan 4 Na Barazanar ɗorewar Wutar Lantarki A Nijeriya – Minista

17 hours ago
GORON JUMA’A 01-07-2025
Labarai

GORON JUMA’A 01-07-2025

19 hours ago
An Zaɓi Saidu Yahya A Matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano
Manyan Labarai

An Zaɓi Saidu Yahya A Matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano

19 hours ago
Next Post
Ruwa

Hajj 2024: Jihar Kaduna Ta Kammala Jigilar Maniyyata Fiye Da 4,000 Zuwa Saudiyya 

LABARAI MASU NASABA

Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa

Ƴansanda Sun Ƙwato Mota Da Aka Sace, Gami Da Cafke Dillalan Ƙwayoyi A Jigawa

August 2, 2025
Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi Haɗin Gwiwa

Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi Haɗin Gwiwa

August 1, 2025
Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine

August 1, 2025
2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa

2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa

August 1, 2025
Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu

August 1, 2025
Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa

August 1, 2025
Sin Ta Samu Bunkasar Tafiye-Tafiye Cikin Gida Da Kashi 20.6% A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Bunkasar Tafiye-Tafiye Cikin Gida Da Kashi 20.6% A Rabin Farko Na Bana

August 1, 2025
Tinubu Ya Sauke Gawuna A Matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwar BUK, Ya Maye Gurbinsa Da Kaita 

Tinubu Ya Sauke Gawuna A Matsayin Shugaban Kwamitin Gudanarwar BUK, Ya Maye Gurbinsa Da Kaita 

August 1, 2025
Majalisar Dokokin Sokoto Ta Aike Wa  Kwamishina Sammaci, Duba Dalili

Majalisar Dokokin Sokoto Ta Aike Wa  Kwamishina Sammaci, Duba Dalili

August 1, 2025
Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Nanata Shan Damarar PLA A Kan Sake Hadewar Kasar

Ministan Tsaron Kasar Sin Ya Nanata Shan Damarar PLA A Kan Sake Hadewar Kasar

August 1, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.